Mun Daina Adawa da Tikitin Musulmi da Musulmi, Shugabannin Kiristoci
- Kiristocin Najeriya sun canza tunani kan adawar da suka yi da tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu da Shettima a zaben 2023
- A wurin wani taro a Abuja, jagororin mabiya addinin Kirista sun ce tsoron da suka ji na haɗa Musulim/Muslim ya gushe
- A cewarsu, shugaba Tinubu da Shettima sun kwatanta adalci da daidaito a naɗe-naɗen da suka yi kawo yanzu
Wasu shugabannin mabiya addinin kirista a Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar NaSA sun bayyana cewa a yanzu fargabar da su ke game da tikitin Musulmi da Musulmi ta gushe.
Sun ce tsoron da suka ji dangane da takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Ƙashim Shettima, ya kau a halin yanzu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Sun ce tsoronsu ya ta’allaka ne kan yiwuwar yi wa Kiristoci zagon kasa da kuma zaluntar su a kasar nan.
Jagororin Kiristocin sun bayyana haka ne a birnin tarayya Abuja a wurin taron kaddamar da kwamitocin wayar da kai da haɗa kan jama'a kan taron da za su yi a watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin, Archbishop Leonard Kawas, ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya musamman mabiya addinin kirista da su tashi tsaye wajen gudanar da azumi da addu’o’i na kwana daya ga kasar nan.
Ya ce azumin kwanaki 40 da aka shirya yi zai fara ne daga ranar 20 ga watan Oktoba kuma a karƙare ranar 30 ga watan Disamba, 2023, kwana ɗaya gabanin babban taron.
Shugaba Tinubu ya kunya ta mutane da dama
Farfesa Bature, Shugaban Catholic Charismatic Renewal of Nigeria, ya ce ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya kunyata ma su tunanin tikitin Musulmi/Musulmi zai jefa kasar nan cikin rikici.
Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa
A cewarsa, Tinubu ya tabbatar da cewa an kwatanta adalci da daidaito wajen naɗa Musulmai da Kiristoci a muƙaman siyasa.
A rahoton Trust Radio, Bature ya ce:
“Daya daga cikin abubuwan da suka haifar da tashin hankali a lokacin zaben da ya gabata shi ne yadda Kiristoci da yawa a Najeriya suka ji tsoron tikitin Musulmi da Musulmi."
"Ya haddasa fargaba mai yawa amma da ikon Allah tsoron ya kau daga zukatan mu. Shugaban kasa da mataimakinsa sun nuna adalci a irin nade-naden siyasa da suka yi."
“Muna gani babu wanda zai fito ya yi kukan wariya saboda Musulmi sun samu nasu kaso, Kirista ma sun samu nasu."
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Oborevwori Na Jihar Delta
A wani rahoton na daban Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta.
A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, Kotun ta kori ƙarar da ɗan takarar gwamna na SDP ya kalubalanci zaɓen.
Asali: Legit.ng