Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Oborevwori Na Jihar Delta

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Oborevwori Na Jihar Delta

  • Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta
  • A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, Kotun ta kori ƙarar da ɗan takarar gwamna na SDP ya kalubalanci zaɓen
  • Daga ƙarshe kuma Kotun Allah ya isa ta yi watsi da ƙarar Chief Kenneth Gbagi bisa cin mutuncin shari'a

Jihar Delta - Kotun ƙolin Najeriya ta yi fatali da ƙarar da ɗan taƙarar gwamnan jihar Delta a inuwar jam'iyyar SDP, Cif Kanneth Gbagi, ya shigar kan zaɓen 18 ga watan Maris.

Kotun, wacce ake wa taken Kotun Allah ya isa ta yanke wannan hukunci ne ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Oborevwori na Delta da ɗan takarar SDP.
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Oborevwori Na Jihar Delta Hoto: Kenneth Gabagi, Rt Hon Sherrif Oborevwori
Asali: Facebook

Meyasa Kotu ta kori ƙarar Gbagi?

Mista Gbagi ya kalubalanci matakin ayyana Gwamna Sherrif Oborevwori na jam'iyyar PDP a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka yi a 2023.

Kara karanta wannan

CSU: Atiku Ya Shiga Matsala, An Roƙi Shugaba Tinubu Ya Cire Masa Lambar Girma Ta GCON

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kwamitin alkalai biyar na Kotun koli karkashin mai shari'a Inyang Okoro, ya tambayi lauyan Gbagi, Akintola, SAN, kan ko Kotun tana da hurumin sauraron karar.

Kotun kolin ta bayyana cewa kwanaki 180 da doka ta ba wa kotun zaɓe damar tantance irin waɗan nan ƙorafe-ƙorafe, ya wuce.

Ta kuma yi watsi da rokon lauyan wanda ya shigar da kara, wanda ya nemi yin amfani da asalin ikon kotun koli a karkashin sashe na 22 na dokokin kotun koli.

A rahoton Daily Independent, Mai shari'a Okoro ya ce:

"Lokacin da aka ɗiba na sauraron wannan batu ya wuce. Idan har Kotun zaɓe ba ta sake bada wani lokacin ba, hakan na nufin wannan Kotun ba zata iya shiga huruminta ba sabida kwanaki 180 sun wuce."
"A halin da ake ciki yanzu, hukuncin karshe na Kotun zaɓe ne kaɗai za a iya ɗaukaka ƙara zuwa gaba, wannan batu ne da ya shafi ilimi."

Kara karanta wannan

Muhimman Matakai 5 Da Gwamna Abba Ya Dauka Bayan Kotu Ta Kwace Nasararsa a Zabe

KWASU: Shugaba Bola Tinubu Ya Kuma Nada Dalibar Jami'a a Mukami

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya ƙara naɗa dalibar jami'a da ke karatun digirin farko a kwamitin tsare-tsaren kasafi da sake fasalin haraji.

Ya naɗa Olamide Obagbemileke, ɗalibar 400-Level da ke karatun tattalin arziki a jami'ar jihar Kwara a matsayin mai taimakawa kan bincike da nazari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262