KWASU: Shugaba Bola Tinubu Ya Kuma Nada Dalibar Jami'a a Mukami

KWASU: Shugaba Bola Tinubu Ya Kuma Nada Dalibar Jami'a a Mukami

  • Bola Ahmed Tinubu ya ƙara naɗa dalibar jami'a da ke karatun digirin farko a kwamitin tsare-tsaren kasafi da sake fasalin haraji
  • Ya naɗa Olamide Obagbemileke, ɗalibar 400-Level da ke karatun tattalin arziki a jami'ar jihar Kwara a matsayin mai taimakawa kan bincike da nazari
  • Wannan naɗi na dalibar jami'a shi ne na biyu a cikin watanni 6 da kama aikin gwamnatin shugaba Tinubu

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa ɗalibar jami'ar jihar Kwara (KWASU), Olamide Obagbemileke, a kwamitin tsare-tsaren kasafi da fasalin haraji.

Ɗalibar 'yar aji huɗu watau 400 Level dai tana karatun ilimin tattalin arziƙi a jami'ar kuma shugaba Tinubu ya naɗa ta a matsayin mai taimaka wa kan bincike da nazari.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ɗalibar KWASU a muƙami.
KWASU: Shugaba Bola Tinubu Ya Kuma Nada Dalibar Jami'a a Mukami Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kwara State University
Asali: Twitter

Jami'ar Kwara (KWASU) ce ta sanar da wannan sabon naɗi na Obagbemileke a shafinta na manhajar X watau tsohuwar Tuwita da yammacin ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

CSU: Atiku Ya Shiga Matsala, An Roƙi Shugaba Tinubu Ya Cire Masa Lambar Girma Ta GCON

Ta ƙara da cewa takardar naɗin ɗalibar na ɗauke da sa hannun Bomate Ogaree-Lawson, mataimaki na musamman ga shugaban kwamitin shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani kan kwamitin shugaban ƙasa na sake fasalin haraji

A ranar 8 ga watan Augusta, Shugaba Tinubu ya kaddamar da wannan kwamitin a fadar shugaban ƙasa, inda ya naɗa Taiwo Oyedele a matsayin shugaban kwamitin.

Haka nan kuma ya naɗa Orire Agbaje, wanda ke aji huɗu watau 400 Level a sashin koyon ilimin tattalin arziƙi a jami'ar Ibadan, jihar Oyo.

Wane aiki ɗalibar KWASU zata yi a kwamitin?

Bisa wannan ci gaban, Obagbemileke ta zama ɗalibar jami'a ta biyu da aka naɗa a kwamitin shugaban ƙasa tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.

Obagbemileke zata yi aiki da kwamitin na tsawon watanni uku a matsayin ambasadar ɗalibai.

Sanarwan ta ce:

Kara karanta wannan

'Ɗan Shekara 15 Da Ya Fi Kowa Cin JAMB Ya Zama Kakakin Majaisar Dokokin Jihar PDP

"Ba ni da shakka cewa himmarki, sadaukarwa, da sabbin ra'ayoyinki za su amfani Kwamitinmu sosai kuma zai taimaka mana wajen cimma burinmu."

Atiku Ya Shiga Matsala, An Roƙi Shugaba Tinubu Ya Cire Masa Lambar Yabon GCON

A wani rahoton kuma Alhaji Atiku Abubakar na shan suka ta ko ina biyo bayan kalaman da ya yi a wurin taron 'yan jarida da ya gudanar ranar Alhamis.

Wannan yunkuri ya jawo wata ƙungiya ta roƙi shugaba Bola Tinubu ya soke karramawar da aka yi wa Atiku ta GCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262