Babban Abin Da Ya Dace Atiku Da Obi Su Yi Kafin 'Karshen Wa'adin Tinubu' Joe Igbokwe Ya Bada Shawara
- Babban dan gani kashenin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Joe Igbokwe, ya ba manyan yan takarar shugaban kasa biyu da ke adawa da sakamakon zaben shugaban kasa da ya gabata
- Legit Hausa ta rahoto cewa Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi sun garzaya kotun koli suna neman a tsige shugaban kasa Tinubu
- Igbokwe ya ce maimakon yin duk mai yiwuwa don tsige shugaban kasa Tinubu daga mulki, kamata ya yi ace Atiku da Obi sun fara kamfen don zabuka biyu masu zuwa
Ikeja, Jihar Lagos - Joe Igbokwe, jigon jam'iyyar APC mai mulki, ya shawarci Atiku Abubakar da Peter Obi a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, cewa su fara shirin zaben 2031.
Legit Hausa ta rahoto cewa da wannan furuci ba Ibokwe, yana nufin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai yi kaka-gida a fadar shugaban kasa na cikakkun shekaru takwas.
Kotun Koli: Wata Sabuwa Yayin da Shararren Malami Ya Yi Hasashen Sabon Zabe Tsakanin Atiku Da Peter Obi
'Ku mayar da hankali kan 2031': Igbokwe ga Atiku da Obi
Jigon na APC ya ce Atiku da Obi, yan takarar shugaban kasa na PDP da LP, "kuna da shekaru takwas na sanar da yan Najeriya wanene ku."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Igbokwe ya bukaci manyan yan adawan biyu da su tallata kansu da nasarorinsu a rayuwa.
Babban Manajan na hukumar samar da ababen more rayuwa ta jihar Legas (LASIMRA) na farko, ya rubuta hakan ne a shafinsa na Facebook.
"Wannan ita ce shawarata ta gaskiya ga wadanda suka fadi zaben shugaban kasar 2023 a Najeriya: Ku je ku fara shirya ma 2031.
"Kuna da shekaru 8 don fada ma yan Najeriya ku wanene: magabatanku, bayananku, tarihin ku, bajintar da kuka yi da kuma nasarorin ku."
“Za ku gani zai zo ya wuce”: Malami ya ce za a sake zabe tsakanin Atiku da Obi
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa Fasto Kingsley Okwuwe na cocin Revival and Restoration Global Mission ya yi hasashen sake zabe tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi.
Fasto Okwuwe ya yi hasashen ne a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, ta shafinsa na YouTube.
A cikin jawabin nasa, malamin addinin ya yi hasashen cewa za a tilastawa Shugaban kasa Tinubu barin kujerar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng