Chikago: Kungiya Ta Shawarci Tinubu Ya Tuɓe Karramawar Atiku Ta GCON

Chikago: Kungiya Ta Shawarci Tinubu Ya Tuɓe Karramawar Atiku Ta GCON

  • Alhaji Atiku Abubakar na shan suka ta ko ina biyo bayan kalaman da ya yi a wurin taron 'yan jarida da ya gudanar ranar Alhamis
  • A taron, ɗan takarar PDP a zaben 2023 ya yi bayanin manufarsa ta zuwa jami'ar jihar Chicago da kuma faɗan da ke tsakaninsa da Tinubu a Kotu
  • Wannan yunkuri ya jawo wata ƙungiya ta roƙi shugaba Bola Tinubu ya soke karramawar da aka yi wa Atiku ta GCON

FCT Abuja - Wata gamayyar kungiyoyi masu fafutukar ganin an gudanar da shugabanci nagari ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tashi tsaye wajen yaƙar Atiku Abubakar.

Ƙungiyar ta roƙi shugaba Tinubu ya tuɓe rigar karramawar da Najeriya ta bai wa Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa

Peter Obi da Atiku.
Chikago: Kungiya Ta Shawarci Tinubu Ya Tuɓe Karramawar Atiku Ta GCON Hoto: Mr Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cewar gamayyar, tana rokon Tinubu ya kudiri aniyar yaƙar Atiku da gaske kuma ya cire lambar girman da aka ba Atiku watau GCON.

Ta ce babu sauran gashin girma ko sili ɗaya a jikin mutumin da ke burin ɓata ofishin shugaban ƙasa saboda siyasar ɓangaranci ta rufe masa ido.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gamayyar dai ta yi nuni da cewa babu wani abu mai daraja a tare Atiku tun da ya yi wadannan zarge-zargen game da sahihanci ko akasin haka na takardar karatun Tinubu a jami'ar CSU.

Kungiyar ta yi magana kan Peter Obi

Da take jawabi a taron yan jarida ranar Talata, shugabar gamayyar ƙungiyoyin CSO, Ene Lilian Ogbole, ta roƙi 'yan Najeriya su yi fatali da kalaman Peter Obi na LP.

Ta ce cirewa Atiku lambar yabo ta kasa, wanda aka saba kebewa ga mataimakan shugaban kasa, zai zama izina ga wasu ta yadda ‘yan Najeriya za su fara ganin ƙimar ofishin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Takardun Karatun da Tinubu, Atiku, Peter Obi, Kwankwaso Suka Ba INEC Kafin Zaben 2023

Dokta Ogbole ta kuma caccaki Mista Obi kan neman sanin taƙamaiman waye shugaba Tinubu, tana mai bayyana hakan a matsayin yarinta, abin kunya da raha.

Dalibin Da Ya Fi Kowa Cin JAMB a Jihar Edo Ya Zama Kakakin Majalisa Na Kwana Daya

A wani rahoton kuma Ɗalibin da ya fi kowa yawan maki a JAMB daga jihar Edo ya zama shugaban majalisar dokokin jihar na kwana ɗaya.

Kakakin majalisar, Blessing Agbebaku, shi ne ya karrama shi da matsayin yayin da aka gabatar masa da ɗalibin ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262