Jerin Manyan Jami'an Gwamnati Da Tinubu Ya Kora Yayin Da Ya Ke Nada Masu Maye Gurbinsu

Jerin Manyan Jami'an Gwamnati Da Tinubu Ya Kora Yayin Da Ya Ke Nada Masu Maye Gurbinsu

A ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, Shugaba Bola Tinubu ya sallami shugabannin wasu hukumomin gwamnati karkashin Ma'aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani.

Tinunu ya sallami Danbatta da wasu shugabannin hukumomin gwamnati
Farfesa Umar Garba Danbatta da wasu shugabannin hukumomin gwamnati da Tinubu ya sallama. Hoto: Prof. Umar Garba Danbatta, Sunday Adepoju, Tukur Funtua
Asali: Facebook

Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa a bangaren watsa labarai ya bayyana hakan cikin wata sanarwa cewa korar da aka musu za ta fara aiki nan take.

Wannan rahoton ya kunshi jerin wadanda umurnin na Tinubu ya shafa a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin hukumomin da abin ya shafa sune:

1. Farfesa Umar Garba Danbatta (NCC)

Shugaba Tinubu ya bada umurnin korar Farfesa Umar Garba Danbatta, wanda shine mataimakin shugaba kuma shugaba a Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).

Kwararren injiniya ne, shugaba, mai tallafawa al'umma kuma mai fafutikan gina kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Jawo Yaron Aminin Buhari, Ya ba Shi Mukami Mai Tsoka a Gwamnati

Shine mataimakin shugaba a cibiyar Digital Bridge Institute (DBI), International Centre for Advance Communications Studies wacce NCC ta kafa a 2004 saboda gina yan Najeriya a bangaren sadarwa na zamani.

An maye gurbin Farfesa Danbatta da Aminu Maida.

2. Sunday Adepoju (NIPOST)

An sanar cewa shugaban kasa ya kori Sunday Adepoju a matsayin shugaban Hukumar Tura Sakonni na Kasa, NIPOST, a ranar Laraba.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Sunday, tsohon dan majalisar tarayya, a matsayin shugaban NIPOST a 2022.

An kuma sanar da Tola Odeyemi a matsayin sabon shugaban NIPOST.

3. Tukur Funtua (NIGCOMSAT)

Tukur Mohammed Lawal Funtua na cikin wadanda Shugaba Bola Tinubu ya sallama nan take.

A shekarar 2022, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Injiniya Tukur Funtua, a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Tauraron Dan Adam na Najeriya, NIGCOMSAT.

Tinubu Ya Nada Shugabanni a Hukumomin NIPOST, NCC, NITDA Da Sauransu

Kara karanta wannan

Idris Alubankudi Saliu: Abubuwa 10 a Game da Sabon Hadimin Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin shugabanni a Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, Hukumar Bunkasa Ilimin Fasahar Sadarwa ta Najeriya, NITDA, da Hukumar Aika Sakonni ta Najeriya, NIPOST.

Sauran hukumomin da aka yi sabbin nade-nade sun hada da Hukumar Kula Da Tauraron Dan Adam (NIGCOMSAT) da Hukumar Kare Bayanan Sirrin Masu Amfani da Intanet ta Kasa (NDPC).

Mai ba wa shugaban kasa shawarwari a bangaren labarai, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164