Kogi 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya Da Shugabannin Matan PDP Sun Koma APC

Kogi 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya Da Shugabannin Matan PDP Sun Koma APC

  • Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya da wasu shugabannin mata sun ƙara kassara jam'iyyar PDP a jihar Kogi
  • Jiga-jigan siyasar tare da dumbin magoya bayansu sun sauya sheka daga PDP zuwa APC yayin da ake dab da zaɓen gwamna
  • Hukumar zaɓe INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamnan Kogi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

Jihar Kogi - Ɗan majalisar wakilan tarayya wanda ya wakilci mazaɓar Idah daga jihar Kogi a baya, Honorabul Ismail Inah Hussein, ya sauya sheƙa daga jam'iyar PDP zuwa APC.

The Nation ta tattaro cewa tsohon ɗan majalisar, wanda aka fi sani da Soul Lover, ya fice daga PDP zuwa APC tare da dandazon magoya bayansa.

Tsohon ɗan majalisar tarayya da wasu jiga-jigai sun koma APC.
Kogi 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya Da Shugabannin Matan PDP Sun Koma APC Hoto: thenation
Asali: UGC

Tun a ranar Jumu'a aka ga Soul Lover ya sanya tufafi masu tutar jam'iyyar APC a garin Ajaka, ƙaramar hukumar Igalamela-Odolu, alamar da ta nuna ya haɗe da jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Soyayyar Damfara: Baturiya Ta Bayyana Yadda Dan Yahoo Yahoo Ya Damfare Ta Kudi Har N122m

Meyasa ya zaɓi shiga APC mai mulki?

Inah, wanda ɗan a mutun PDP ne, ya danganta matakin da ya dauka na komawa jam’iyyar APC da burinsa na bada da gudunmawa ga ci gaban jihar Kogi da kasa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello, ta gina hadin kai, tsaro da ci gaba mai dorewa jihar baki daya.

A cewarsa, bisa haka ya ga ya dace ya goyi bayan ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Alhaji Usman Ododo, domin ya ci gaba da ayyukan alheri ga jama'a.

Jiga-Jigan shugabannin matan PDP sun bi sahunsa zuwa APC

Bugu da ƙari, tsohuwar shugabar matan jam’iyyar PDP a karamar hukumar Igalamela, da kuma shugabannin mata na gundumomin yankin duk sun koma APC.

A nasa jawabin, Kwamishinan Sufuri na Kogi, Baron Okwoli, ya yabawa Inah da mabiyansa bisa matakin da suka dauka na shiga APC tare da tabbatar da cewa za su hada kai don ganin jam’iyyar ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

Mataimakin dan takarar gwamna, Joel Oyibo, ya ce ya ji matuƙar daɗi ganin yadda jama'a suka fito kwansu da ƙwarƙwata a wurin bikin karbar tsohon dan majalisar.

Ya bayyana cewa halartar taron alama ce da ke nuna cewa mutane sun yi amanna da APC duk da farfagandar da jam’iyyun adawa ke yi, Sunnews ta rahoto.

Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA

A wani rahoton kuma Wani babban jigon jam'iyyar APC daga ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi, Yahaya Ododo, ya sauya sheƙa zuwa Action Alliance (AA).

Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da daidaito,.gaskiya da adalci a kujerar gwamnan jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262