Atiku Abubakar Ya Gindaya Sharadin da Zai Sa Ya Daina Faɗa da Shugaba Tinubu

Atiku Abubakar Ya Gindaya Sharadin da Zai Sa Ya Daina Faɗa da Shugaba Tinubu

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba gudu ba ja da baya a faɗan da ya kinkimo tsakaninsa da shugaba Bola Tinubu a Kotu
  • Ɗan takarar PDP a zaben shugaban ƙasa 2023 ya ce ba zai taɓa hakura ya janye ba har sai Kotun ƙoli ta yanke hukunci
  • Ya kuma tabbatar da cewa Tinubu ya turo wasu gwamnoni su zauna da shi bayan kammala zaben watan Fabrairu

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya gindaya sharaɗi ɗaya wanda zai sa ya haƙura ya daina “yakin” da yake yi da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Atiku wanda ya zo na biyu a zaben 2023, ya kalubalanci nasarar da Tinubu ya samu a kotu, amma ya sha kaye yayin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi fatali da karar da ya shigar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: "Ban Ci Amanar Shugaba Tinubu Ba" Atiku Ya Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Faru Tsakaninsu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar Ya Gindaya Sharadin da Zai Sa Ya Daina Faɗa da Shugaba Tinubu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Zargin shugaba Tinubu da amfani da takardun karatu na jabu na daya daga cikin wadanda kotun zaben shugaban kasar ta yi watsi da su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Duk da haka, Atiku ya durfafi kotun Amurka, wanda a karshe ta bayar da umarnin a damƙa masa takardun Tinubu, ɗan takarar na PDP na shirin shigar da su a ƙarar da ya ɗaukaka zuwa kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi zargin cewa akwai wata manaƙisa a cikin takardar shaidar da Tinubu ya mika wa hukumar zabe INEC wanda hakan ka iya haramta masa tsayawa takara.

Sharaɗin da zai sa da daina takun saƙa da Tinubu - Atiku

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, 2023, Atiku ya ce bai shirya ja da baya a faɗan da ya kinkimo ba.

Kara karanta wannan

Lauyan Atiku Ya Bayyana Abubuwan Da Suka Bankado Dangane Da Takardun Karatun Da Tinubu Ya Gabatarwa INEC

Vanguard ta tattaro Atiku na cewa:

“Na riga da na shigar da kararsa a gaban kotun koli. Ba zan haƙura ba har sai kotu ta yanke hukuncin cewa shi ke da gaskiya sannan zan janye wannan faɗan."
"Ma’ana zan janye wannan fada idan kotu ta yanke hukunci saboda babu wata kotu da ke sama da kotun koli”.

Da aka tambaye shi ko yana fuskantar matsin lamba daga Tinubu kan ya janye karar, Atiku ya ce bayan zabe ya samu labarin cewa shugaban kasa ya turo tawagar gwamnoni domin su tuntube shi.

Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Ba Su Halarci Taron da Atiku Ya Gudanar Ba

A wani rahoton kuma Manyan shugabannin PDP na ƙasa ba su halarci taron da Atiku Abubakar ya gudanar kan Bola Tinubu ba.

Rashin halartar masu ruwa da tsaki a PDP ya ƙara nuna rabuwar kai da rigingimun cikin gida na ci gaba da ruruwa a.jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262