Majalisa Ta Fara Tantance Mutane 3 Da Tinubu Ya Tura Don Nadin Minista
- A yau Laraba 4 ga watan Oktoba Majalisar Dattawar Najeriya ta fara tantance mutane uku da Shugaba Tinubu ya tura mata don nada su minista
- Mutanen da za a tantance sun hada da Abbas Balarabe daga jihar Kaduna, sai Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande
- Opeyemi Bamidele, jagorar majalisa ne ya gabatar da kudirin fara tantance wadanda za a nada ministocin bayan sun iso zauren majalisa
Majalisar Dattawar Najeriya ta fara tantance mutane uku da za a nada ministoci a kasar, rahoton The Cable.
Wadanda aka tura sunayensu sune Abbas Balarabe, Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya nada Ibrahim da Olawande a matsayin ministan matasa da kuma karamin ministan matasa a watan Satumba.
An samu gibi a kujerar ministan matasa bayan shugaban kasa ya mayar da Abubakar Momoh zuwa Ma'aikatar Cigaban Neja Delta.
Abbas, wanda ya fito daga jihar Kaduna, shine zai zama minista da aka zabo daga jihar ta Kaduna.
Da farko, an zabi Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna a matsayin minista amma majalisa ta gaza tantance shi saboda dalilai da suke da alaka da tantancewa daga hukumomin tsaro.
Bukatar da shugaban kasar ya tura na tabbatar da nadin ministocin na cikin sahsi na 147(2) na kudin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima.
An fara tantancewar a ranar Laraba bayan Opeyemi Bamidele, jagorar majalisa ya gabatar da kudirin fara yin hakan.
Kwamitin da aka dora wa alhakin tantance ministocin ta dukufa ta fara aiki.
A halin yanzu wadanda za a tantance din suna cikin zauren majalisa.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng