Abdullahi Adamu Ya Bayyana Abin Da Tinubu Ya Gaya Masa Bayan Ya Yi Murabus
- Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi magana a karon farko tun bayan barin ofis
- Adamu wanda ya yi murabus bayan rikici ya dabaibaye jam'iyyar, ya ce ya ji daɗi Shugaba Tinubu ya yi nasara
- Tsohon shugaban na APC ya yi nuni da cewa Allah ne ya yi nufin cewa Bola Tinubu sai ya shugabanci ƙasar nan
FCT Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi magana kan wata tattaunawa da suka yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu bayan ya yi murabus a farkon shekarar nan.
Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na ƙasa a babban taron jam'iyyar a watan Maris na 2022, ya sauka ne bisa ƙashin kansa a lokacin rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.
Tinubu ya fita ƙasar waje domin halartar taron kungiyar ƙasashen Afrika, kuma kafin dawowarsa, Abdullahi Adamu ya miƙa takardar murabus ɗinsa, wanda hakan ya share fagen fitowar tsohon gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a matsayin wanda zai gaje shi.
Adamu ya ji daɗi Tinubu ya ci zaɓe
Daily Trust ta ce da yake magana a wata hira da aka yi da shi a shirin Reminiscence, wani shirin gidan talabijin na Trust TV, Adamu ya ce duk da abin da mutane za su ce, ya ji daɗin yadda Tinubu ya lashe zaben lokacin yana shugaban jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Ban yi nadama ba. Abin da ya sa ban yi nadama ba shi ne, abin da Allah ya nufa ne kawai zai faru... Allah ya sa Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar nan."
"A lokacin da ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, na jagoranci kwamitin gudanarwa na ƙasa zuwa gidansa domin taya shi murna tare da ba shi tabbacin cewa za mu tsaya kai da fata tare da shi domin yin aiki wajen samun nasarar jam'iiyyar, kuma mun yi."
Menene abin da Tinubu ya gaya masa?
Tsohon shugaban ya cigaba da cewa:
"Ko me wani zai ce dangane da dangantaka ta da Tinubu, gaskiyar magana ita ce a ƙarƙashin jagorancina ne APC ta ci zabe. Ina son Tinubu saboda abu ɗaya. Lokacin da na gan shi na ƙarshe bayan na yi murabus, ya kira kansa da 'wannan jaririn da ka haifa', hakan ya sanya na ji daɗi."
Gwamna Ahmed Aliyu Ya Yi Nasara
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta tabbatar da nasarar da gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen 2023.
Kotun ya yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta suka shigar suna ƙalubalantar nasarar gwamnan a zaɓen.
Asali: Legit.ng