Kotun Zaben Kano: Kungiya Ta Yi Kira Ga Goyon Baya Da Kare Alkalai Yayin da NNPP Ta Yi Barazana
- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen jihar Kano na fuskantar matsin lamba tun bayan hukuncin kotun zabe
- An zargi NNPP da yin barazana da tsoratar da kwamitin mutum uku na kotun zaben
- Kungiyar Stand Up Nigeria (SUN) ta bukaci shugabancin NNPP da su fito fili su janye barazanarsu sannan su ba alkalan hakuri
FCT, Abuja - Biyo bayan hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano, an bukaci jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da ta sake dabara sannan ta shirya ma zabe na gaba.
Kungiyar Stand Up Nigeria (SUN) ce ta yi wannan kira a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, rahoton The Cable.
An tattaro cewa an shirya taron ne domin magance hare-haren baya-bayan nan da aka kai wa bangaren shari'a, bayan yanke hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano wanda ya kai ga tsige Gwamna Abba Yusuf na NNPP.
Da yake magana a taron, shugaban kungiyar na kasa, Patriot Sunday Attah, ya jinjinawa kwamitin mutum uku na kotun zaben kan yanke hukunci cike da karfin gwiwa duk da matsin lambar da suka fuskanta daga NNPP, rahoton Nigerian Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Attah ya bayyana hukuncin a matsayin izina ga yan siyasar da ke karya doka da oda ba tare da la’akari da hakkokin yan adam ba.
Attah ya ce:
"Ba dole sai kun tsoratar da bangaren shari'a ko kuma ku haifar da yaki saboda kun fadi zabe ba. Wa'adin mulki shekaru hudu ne kawai inda bayan haka za a sake gudanar da sabon zabe.
"Kuna iya shirya kanku don sake tsayawa takara a maimakon daukar nauyin mutane don bata sunan alkalan kotun sauraron kararrakin zabe da ake mutuntawa sosai tare da tsoratar da alkalan kotun daukaka karar gaba daya a wani yunkuri na sauya hukuncin da aka riga aka yanke."
Kungiya ta goyi bayan alkalan kotun zaben Kano
Attah ya bukaci yan Najeriya da su karfafawa alkalan gwiwa tare da goyon baya da kare su a yayin da suke tattare da tashin hankali da fuskantar barazana."
Kungiyar ta bukaci jam’iyyar NNPP da ta fito fili ta janye barazanar da take yi wa alkalai da kuma bangaren shari’a.
"Dole ne yan Najeriya su karfafa alkalai gwiwa tare da goyon bayansu yayin da suke yanke hukunci mai mahimmanci da zai karfafa dimokuradiyyarmu.
"Ya zama dole jam'iyyar NNPP da gwamnatinta su fito fili su janye muguwar barazanar da magoya bayanta ciki harda kwamishinan Abba Kabir Yususf suka yi."
Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu a zaben gwamnan Sokoto
A wani labarin, mun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta yi watsi da ƙarar da dan takarar jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya shigar gabanta kan nasarar da gwamna Ahmed Aliyu ya yi a zaɓen da aka yi ranar na 18 ga watan Maris, cewar rahoton Daily Trust.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana gwamna Ahmed Aliyu, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma Umar ya ƙalubalanci nasarar da ya samu bisa zargin mataimakinsa da gabatar da takardun bogi da tafka maguɗi a zaɓen.
Asali: Legit.ng