Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam’iyyar APGA Kan Gwamnan APC
- Kotun zaben gwamnan jihar Ebonyi ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar APGA da dan takararta suka shigar gabanta dangane da nasarar Gwamna Francis Nwifuru
- Kotu ta yi watsi da karar da ke kalubalantar nasarar gwamnan na jam'iyyar APC
- Ta ce gaba jam'iyyar APGA da dan takararta, Bernard Odoh basu da hurumi a cikin karar da suka shigar don haka ta yi watsi da shi
Jihar Ebonyi - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ebonyi ta yanke hukunci a kan karar da jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) da dan takararta a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Bernard Odoh suka shigar a kan Gwamna Francis Nwifuru.
APGA da Odoh sun shigar da kararraki suna masu kalubalantar nasarar Gwamna Nwifuru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Nwifuru na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, rahoton Punch.
Kotu ta yi watsi da karar APGA kan nasarar gwamnan Ebonyi
Odoh ya yi korafi ta hannun lauyansa, Jibrin Okutepa, SAN, cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Nwifuru wanda ya kasance dan majalisar wakilan jihar Ebonyi kuma kakakin majalisar jihar a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party har zuwa lokacin zaben bai cancanci tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Ebonyi ba."
Sakamakon haka, APGA da Odoh sun bukaci kotun da ta soke nasarar Mista Nwifuru saboda rashin cancantarsa a zaben.
Sai dai kuma, da yake zartar da hukunci, kwamitin kotun zaben mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a Lekan Ogunmoye, ya riki cewa masu karar basu da hurumin shigar da karar saboda lamarin na cikin gida ne na jam'iyyar APC.
Kotun ta bayyana cewa gaba daya bukatun da APGA da dan takararta suka gabatar ya fada ne kan lamuran da suka shafi kafin zabe sannan ta yi watsi da ikirarin masu karar, rahoton The Nation.
INEC ta nuna damuwa kan yanayin tsaro a jihohin Kogi da Imo gabanin zaben gwamna
A wani labarin, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta nuna damuwa matuƙa dangane da yanayin matsalar tsaro a jihohin Kogi da Imo.
Hukumar ta bayyana damuwa kan lamarin ne yayin da take shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni a jihohin guda biyu nan da 'yan watanni.
Asali: Legit.ng