Kotu Ta Kori Karar PDP da Sandy Onor Kan Zaben Gwamnan Jihar Cross River
- Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu na jam'iyyar APC
- Kwamitin alkalan Kotun, yayin yanke hukunci ranar Talata, ya kori ƙarar jam'iyyar PDP da ɗan takararta bisa rashin cancanta
- Hukumar zaɓe ta ayyana Otu a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Kuros Riba da ke Kudu maso Kudancin Najeriya a zaben 18 ga watan Maris, 2023
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Cross River - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kuros Riba ta kori karar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Sandy Onor, suka shigar gabanta.
Kotun ta kori kararrakin da suka kalubalanci nasarar gwamna Bassey Otu na jam'iyyar APC a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Yadda Kotu ta yanke hukunci yau Talata
Kwamitin alkalan Kotun sun bayyana haka ne yayin zaman yanke hukunci wanda ya gudana ranar Talata, 26 ga watan Satumba, 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Alkalan Kotun, sun kori ƙarar PDP da Mista Onor ne saboda ba ta cancanta ba.
Ɗan taƙarar gwamna a inuwar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Otu na APC, wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Kuros Riba.
A sakamakon da hukumar zaɓe INEC ta bayyana bayan kammala zaɓe a jihar da ke Kudu maso Kudu, Otu ya samu ƙuri'u 258,619, yayin Onor na jam'iyyar PDP ya tashi da ƙuri'u 179,636.
Ɗan takarar jam'iyyar APC ya samu nasara a ƙananan hukumomi 15 daga cikin 18 da INEC ta tattara sakamakonsu a Kalabar, babban birnin jihar Kuros Riba.
A halin yanzun, Kotun zabe ta ƙara tabbatar da nasarar Gwamna Otu bayan ta kori ƙarar PDP da ɗan takararta saboda rashin cancanta, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Shugabar Karamar Hukumar da Ya Takali Faɗa da Gwamnan APC Ya Shiga Sabuwar Matsala
A wani rahoton mun kawo muku cewa Kotu ta umarci a garƙame tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun a gidan gyaran hali.
Hakan ya biyo bayan gurfanar da shi da hukumar 'yan sanda ta yi a gaban Kotun majistire mai zama a Abeokuta ranar Talata.
Asali: Legit.ng