NNPP Ta Yi Martani Ga Hukuncin Kotun Zaben Kano Da Ta Tsige Abba Gida Gida
- Shugabancin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party bata ji dadin hukuncin kotun zaben jihar Kano ba
- Jam’iyyar NNPP a cikin wata sanarwa daga mukaddashin shugabanta na kasa, Abba Kawu Ali, ta ce hukuncin da kotun zaben ta yanke rashin adalci ne
- Jam’iyyar adawa a jihar Kano ta zargi kotun zaben da zalunci ta hanyar rage yawan kuri’u daga sakamakon NNPP domin ganin APC ta yi nasara a hukuncin da ta yanke
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, (NNPP) ta bayyana hukuncin kotun zaben jihar Kano da ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf, a matsayin "rashin adalci".
NTA News ta rahoto cewa mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Abba Kawu a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi zargin cewa saboda rashin adalci, kotun zaben ta cire kuri'u 165,663 daga sakamakon jam'iyyar don jam'iyyar APC mai mulki ta samu nasara.
Da yake rokon a kwantar da hankula a jihar Kano, mukaddashin shugaban ya kuma yi zargin cewa hukuncin cin zarafi ne ga kundin tsarin mulki, yana mai shan alwashin cewa za su daukaka kara a kan hukuncin.
Jaridar Punch ta rahoto cewa NNPP ta yi ikirarin cewa hukuncin kotun zaben ya maimaita abun da aka yi a zaben gwamnan na 2019, inda kotun zaben ta murde kuri'un mutane tare da bayar da shi ga wanda ya fadi zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan hukuncin kotu: An saka dokar kulle na awanni 24 a jihar Kano
A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa an saka dokar kulle na awanni 24 a jihar Kano sakamakon hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf. Hukuncin ya fara aiki daga karfe 6:00 na yammacin Laraba.
Kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, a cikin wata sanarwa da ya sawa hannu, ya ce an baza tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa a fadin jihar don tabbatar da bin dokar kullen.
Gumel ya ce wannan matakin ya biyo bayan umurnin da suka samu ne daga gwamnatin jihar a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya a gaba daya jihar.
Asali: Legit.ng