Lauya Ya Maida Martani Ga Tinubu Kan Nada Gwamnan Babban Banki CBN
- Lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Festus Ogun, ya ayyana matakin shugaba Tinubu ya naɗa sabon gwamnan CBN da saɓa doka
- Ya ce Bola Ahmed Tinubu ba shi da ikon naɗa gwamnan CBN yayin da har yanzu ba a cire Emefiele da aka dakatar ba ko ya yi murabus
- A ranar Jumu'a, Bola Tinubu ya amince da naɗa Olayemi Cardoso tare da mataimakan gwamna 4 gabanin majalisa ta tantance su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Wani lauya a Najeriya, Festus Ogun, ya caccaki shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa naɗa Dokta Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Masanin dokokin ya soki matakin shugaban ƙasar ne a shafinsa na manhajar X (watau Tuwita a baya) ranar Jumu'a, 14 ga watan Satumba, 2023.
Lauyan ya bayyana naɗin Dokta Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN da wanda ya saɓa wa doka da kuma yi wa kundin tsarin mulki hawan ƙawara.
Idan baku manta ba a ranar Jumu'a (Jiya) shugaba Tinubu ya amince da naɗin Cardoso da mataimakan gwamnan CBN guda huɗu da zaran majalisar dattawa ta tantance su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tinubu ya saɓa wa doka - Ogun
Da yake maida martani, Mista Ogun ya ce bai dace Tinubu ya nada Cardoso ba yayin da har yanzu ba a kori Godwin Emefiele, gwamnan CBN da aka dakatar ba, kuma bai yi murabus ba.
"Nada sabon Gwamnan CBN a lokacin da "Gwamnan CBN da aka dakatar" tun da farko ba a tsige shi ba, kuma bai yi murabus ba, ya sabawa doka da kundin tsarin mulki."
Idan zaku iya tuna wa, shugaba Tinubu ya dakatar Emefiele daga matsayin gwamnan CBN, kuma awanni bayan haka hukumar tsaron farin kaya ta damƙe shi.
Har yau Emefiele na hannun DSS kuma babu wani sahihin bayani da ya nuna ya yi murabus daga muƙaminsa na gwamnan CBN ko kuma an tsige shi.
Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Hadimai 136 a Gwamnatinsa
A wani rahoton na daban Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya amince da naɗa sabbin hadimai 136 a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
Gwamnan ya bayyana haka ne da daren ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba, 2023 a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Gyang Bere.
Asali: Legit.ng