Zaben Imo: Karin Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar APC ta ƙara kassara babbar jam'iyyar adawa PDP yayin da ake tunkarar zaben gwamna a jihar Imo
- Tawagar ƙarin jiga-jigan mambobin PDP a yankin ƙaramar hukumar Ohaji-Egbema sun sauya sheƙa zuwa APC
- Shugaban APC na jihar Imo ya ja hankalin masu sauya sheƙar su yi aiki tukuri domin nasarar gwamna Uzodinma a zabe na gaba
Jihar Imo - Jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara maraba da sabbin mambobi yayin da jam'iyyar PDP ƙe ƙara rushe wa a garin Egbema, ƙaramar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo.
The Nation ta tattaro cewa masu sauya sheƙar sun sha alwashin haɗa kai da sauran mambobin APC wajen goyon bayan tazarcen gwamna Hope Uzodinma a zaɓe mai zuwa.
Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 domin gudanar da zaɓen gwamna a jihar Imo, Kogi da kuma Bayelsa, Channels tv ta rahoto.
Meyasa suka sauya sheka daga PDP zuwa APC?
Sun ƙara da bayanin cewa matakin barinsu PDP da shiga APC ya samo asali ne daga burinsu na ba da gudummuwa domin tabbatar da tazarcen gwamna mai ci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi ga sabbin mambobin daga Egbema, Mista Opiah ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP daga Ohaji-Egbema za su sauya sheka zuwa APC.
Ya ce:
"Akwai wadanda har yanzu suna ɗan kokwanto amma nan ba da jimawa ba za su yanke shawara. Burin mu ne mu ruguza jam’iyyar PDP a Ohaji-Egbema domin gwamna ya yi tazarce."
APC ta buƙaci aiki tukuru daga mambobin
Shugaban APC na Imo, Mcdonald Ebere, yayin da yake maraba da masu sauya shekar, ya bukace su da su yi aiki tukuru domin tabbatar da gwamna Uzodinma ya yi nasara.
Mista Ebere ya ce:
"Kuna ganin muna karbar ku ana cikin ruwan sama. Wannan ya nuna da gaske muke, a shirye muke mu karɓe ku a kowane lokaci. Ina rokon ku da ku yi aiki tukuri domin gwamna ya yi nasara."
Bola Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya
A wani rahoton kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Aliyu Tijani Ahmed a matsayin sabon shugaban hukumar kula da baƙi da 'yan gudun hijira ta ƙasa
Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da wannan naɗi ne a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023.
Asali: Legit.ng