Kotun Zabe Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule a Jihar Nasarawa
- Kotun zaɓe mai zama a Lafia, babban birnin Nasarawa ta tanadi hukunci kan sahihincin nasarar gwamna Sule a zaben 2023
- Ɗan takarar jam'iyyar PDP ya shaida wa Kotu cewa shi ya samu ƙuri'u mafi rinjaye amma INEC ta bayyana sakamako na daban
- A zaman karshe ranar Alhamis, Lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun roƙi Kotu ta kori ƙarar saboda rashin cancanta
Nasarawa - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna mai zama a Lafia, jihar Nasarawa ta tanadi hukuncin ƙarar da ta kalubalanci sakamakon zaben jihar a 2023.
Hukumar dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, David Ombugadu, shi ne ya kalubalanci nasarar gwamna Abdullahi Sule na APC.
Kotun ta tsara zaman yau Alhamis domin karɓan rubatattun bayanan karshe daga Lauyan mai ƙara da kuma lauyoyin waɗanda ake tuhuma na ɗaya, na biyu da na uku.
Daily Trust ta ce shugaban kwamitin alƙalan kotun, mai shari'a Ezekiel Ajayi, ya jingine yanke hukunci zuwa nan gaba bayan kowane ɓangare ya gabatar da bayanansa na ƙarshe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce Ƙotu zata sanar da kowane ɓangare ta hannun lauyoyinsu da zaran ta sanya ranar yanke hukunci, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Yadda zaman Kotun ya ƙarƙare
Tun da farko, Kanu Agabi (SAN), jagoran Lauyoyin masu shigar da kara, ya shaidawa kotun cewa ya amince da dukkan hujjojin a cikin rubutaccen jawabin ƙarshe.
Lauyan ya bukaci kotun da ta soke zaben gwamnan jihar Nasarawa saboda rashin bin dokar zabe tare da bayyana dan takarar PDP a matsayin sahihin wanda ya samu nasara.
Agabi ya kuma ƙara cewa babu wata alaka tsakanin kuri'u aka gani a IREV da sakamakon karshe da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana.
Lauyan mai shigar da kara ya ce dan takarar PDP ne ya fi yawan kuri’un da aka kada a zaben, bisa ga bayanan da ke cikin IREV da bayanan na’urorin BVAS da aka yi amfani da su a rumfunan zabe daban-daban.
A bangarensu, lauyoyin INEC, APC, da Gwamna Sule, Mista Isiaka Dikko (SAN), Hassan Liman (SAN) da Wole Olanikpekun (SAN), sun miƙa jawaban karshe a rubuce, kana suka yi kira ga kotun ta yi watsi da karar bisa rashin cancanta.
Ƙotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP
A wani labarin kuma kun ji cewa yayin da Kotun zaɓe ke ci gaba da yanke hukunci kan kujerun siyasa, da alamu hukuncin zaɓen gwamnoni na dab da fara fitowa
Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben jihar Ribas ta tanadi hukuncin da zata yanke kan karar da ta kalubalanci nasarar gwamna Fubara.
Asali: Legit.ng