Kotu Ta Kori Karar Dan Takarar Labour Party Kan Sanatan Kaduna Ta Kudu Na PDP

Kotu Ta Kori Karar Dan Takarar Labour Party Kan Sanatan Kaduna Ta Kudu Na PDP

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Kaduna ta yi hukunci kan ƙarar zaɓen Sanatan Kaduna ta Kudu
  • Kotun ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Michael Auta, ya shigar kan nasarar Sanata Sunday Marshall na PDP
  • Alƙalan kotun sun yi fatali da ƙarar bisa rashin kawo gamsasssun hujjoji da wanda ya shigar da ƙarar ya yi

Jihar Kaduna - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a jihar Kaduna, ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar sanatan Labour Party na Sanatan Kaduna ta Kudu, Michael Auta ya shigar, cewar rahoton The Punch.

Auta ya shigar da ƙarar ne yana neman kotun da ta soke nasarar Sanata Sunday Marshall na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), rahoton The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP, Ta Yi Fatali Da Karar Yan Takarar APC Da LP

Kotu ta kori karar dan takarar LP kan sanatan Kaduna ta Kudu
Sanata Sunday Marshall ya yi nasara a kotu Hoto: Barr. Sunday Marshall Katung
Asali: Facebook

Kotu ta zartar da hukuncinta

Kotun mai alƙalai uku a hukuncin da ta yanke, ta bayyana cewa ɗan takarar na Labour Party ya kasa kawo ƙwararan hujjoji kan zargin da yake yi na cewa zaɓen ba a gudanar da shi kan tanadin sabuwar dokar zaɓe ba, da rikici a lokacin zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin ƙararsa, Auta ya yi zargin cewa zaɓen an gudanar da shi bisa rashin bin tanadin dokokin zaɓe ba, sannan ba a gudanar da zaɓe ba a wasu sassan ƙananan hukumomin Kachia da Kagarko, inda ya buƙaci a soke ayyana Marshall a matsayin wanda ya yi nasara da hukumar INEC ta yi.

Ɗaya daga cikin alƙalan wanda ya zartar da hukuncin, mai shari'a O.O. Oluboyede, ya bayyana cewa mai shigar da ƙarar ya kasa kawo gamsassun hujjoji domin tabbatar da ƙarar da ya shigar. Sai ya yi fatali da ƙarar gaba ɗayanta.

Kara karanta wannan

Gaya vs Sumaila: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Sanatan Kano Ta Kudu

Ɗaya daga cikin lauyoyin wanda ake ƙara, Zigwai Z. Adamu, ya bayyana cewa ɗan takarar na Labour Party a cikin ƙararsa ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓe a wasu rumfunan zaɓe ba, amma ya kasa kawo ƙwarararan hujjoji kan zargin da yake yi.

Sanatan PDP Ya Yi Nasara a Kotu

A wani labarin kuma, sanatan jam'iyyar PDP na Enugu ta Yamma, Injiniya Osita Ngwu ya samu nasara a kotun zaɓe.

Kotun zaɓen mai zamanta a birnin Enugu ta yi fatali da ƙararrakin da abokan takararsa suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng