Kotun Zaben NASS Ta Tsige Sanatan Jam'iyyar APC a Jihar Delta

Kotun Zaben NASS Ta Tsige Sanatan Jam'iyyar APC a Jihar Delta

  • Kotun zaɓe ta bayyana zaben Sanatan mazaɓar jihar Delta ta tsakiya na APC a matsayin wanda bai kammalu ba watau Inconclusive a turance
  • Kwamitin alkalan Kotun ya umarci INEC ta gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 4 cikin 8 da ke mazaɓar
  • Ɗan takarar PDP ne ya kai ƙara Kotu, inda ya nemi a kwace kujerar a ba shi ko kuma a karisa zaɓe a kananan hukumomi 4

Jihar Delta - Kotun sauraron ƙararrakin zaben majalisar tarayya mai zama a Asaba ta ayyana zaben Sanatan ta tsakiya na ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kwamitin alƙalai uku na Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a W.I. Kpochi, ya ba da umarnin ƙarisa zaɓe a rumfunan zaɓe 48 a ƙananan hukumomi 4 daga cikin 8 na mazaɓar.

Jam'iyyar APC ta rasa ƙarin kujerar Sanata a jihar Delta.
Kotun Zaben NASS Ta Tsige Sanatan Jam'iyyar APC a Jihar Delta Hoto: punchng
Asali: Twitter

Ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta janye takardar shaidar cin zaɓen da ta bai wa Sanata Ede Dafinone na jam'iyyar APC, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Rushe Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar APC, Ta Ayyana Zaɓen a Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba

Tun da farko, ɗan takarar Sanatan mazaɓar Delta ta tsakiya a inuwar jam'iyyar PDP, Ighoyota Amori, ne ya garzaya ya shigar da ƙara Kotun bayan INEC ta ba APC nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya roƙi kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen wanda ya lashe zabe ko kuma idan haka ba ta samu, ta yi umarnin ƙarisa zaɓe a ragowar kananan hukumomi 4, The Cable ta tattaro.

Yadda Kotu ta kwace nasarar APC a Delta

Idan baku manta ba a makon da ya gabata, Kotun sauraron kararrakin zaben NASS ta bayyana zaɓen Sanata Joel Onowakpo na APC a mazaɓar Delta ta kudu a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kotun ta kuma umarci hukumar zaɓe INEC ta shirya ƙarishen zaɓen a yankin ƙaramar hukumar Warri ta arewa cikin kwanaki 90 masu zuwa, Ripples ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Zaben NASS Ta Tsige Ɗan Minista Daga Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya, Ta Ba Da Sabon Umarni

Haka zalika Kotu ta tabbatar da nasarar Benedict Etanabene na Labour Party a matsayin zababben ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Okpe/Sapele/Uvwie.

Kotun Zabe Ta Ayyana Zaben Ɗan Majalisar Tarayya A Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba

A wani rahoton kuma Kotun zaɓen NASS mai zama a jihar Legas ta soke sakamakon zaben ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Eto Osa.

Ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 33 da zabe bai gudana ba cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262