Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Kabiru Gaya Na APC Kan Sanata Kawu Sumaila Na NNPP

Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Kabiru Gaya Na APC Kan Sanata Kawu Sumaila Na NNPP

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Kano, ta zartar da hukunci kan ƙarar zaɓen sanatan Kano ta Kudu
  • Kotun ta yi fatali da ƙarar da Kabiru Gaya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP
  • A cewar mai shari'a R.O Odogu kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta inda ta umarci mai shigar da ƙara ya ba wanda ake ƙara N200,000

Jihar Kano - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a birnin Kano, babban birnin jihar Kano ta yi watsi da ƙarar Kabiru Ibrahim Gaya na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Kabiru Gaya ya shigar da ƙarar ne yana ƙalubalantar nasarar da Abdulrahman Kawu Sumaila na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya samu a zaɓen sanatan Kano ta Kudu.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Zaben 'Yar Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Ba Dan Takarar APC Nasara

Kotu ta kori karar Kabiru Gaya kan Kawu Sumaila
Kotu ta tabbatar da nasarar Kawu Sumaila a zaben sanatan Kano ta Kudu Hoto: Senator Kabiru Gaya, Sen. S.A Kawu Sumaila
Asali: Facebook

Meyasa kotu ta yi fatali da ƙarar?

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta, cewar rahoton Daily Trust.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun mai alƙalai uku wacce mai shari'a R.O. Odogu yake jagoranta ta yi hukunci cewa mai shigar da ƙarar ya kasa sauke nauyin da ke kansa na kawo hujjoji akan wanda ya lashe zaɓen.

Mai shari'a Odogu ya bayyana cewa sun yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta, rahoton Leadership ya tabbatar.

A kalamansa:

"Ba mu ga wata cancanta a cikin wannan ƙarar ba, saboda haka, mun yi watsi da ita. Hakazalika mun sake tabbatar da ayyana Abdulrahman Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairun 2023."

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da LP, Kotun Zaɓen NASS Ta Yanke Hukunci

"Kotu ta kuma umarci masu shigar da ƙara su biya waɗanda ake ƙara tsabar kuɗi N200,000."

Kotu Ta Tsige Dan Majalisa NNPP

A wani labarin kuma, Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya ta ƙwace nasarar Idris Dankawu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) daga kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kumbotso ta jihar Kano.

Kotun zaɓen ta soke zaɓen Dankawu ne bisa ƙirkirar takardar jarrabawarsa ta WAEC wacce ya gabatar domin shiga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel