Niger: Ɗan Minista Ya Rasa Kujerarsa Ta Dan Majalisar Tarayya a Kotu

Niger: Ɗan Minista Ya Rasa Kujerarsa Ta Dan Majalisar Tarayya a Kotu

  • Kotun zaɓe mai zama a jihar Neja ta rushe nasarar ɗan tsohon Ministan yaɗa labarai wanda ya ci zaben ɗan majalisar tarayya
  • Kwamitin alƙalan Kotun sun soke sakamakon wasu rumfunan zaɓe kana suka umarci INEC ta shirya sabon zaɓe don tantance wa
  • Ɗan takarar jam'iyyar APC ne ya kai ƙara Kotu bisa hujjar cewa an saɓa wa kundin dokokin zaɓe

Niger - Kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majisun tarayya da na jiha ta jihar Neja ta tsige Joshua Gana daga kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya.

Joshua, ɗan tsohon ministan yaɗa labarai, Jerry Gana, shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP na mazaɓar Edati/Lavun/Mokwa ta tarayya a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Tsohon Minista, Jerry Gana tare da ɗansa.
Niger: Ɗan Minista Ya Rasa Kujerarsa Ta Dan Majalisar Tarayya a Kotu Hoto: thecable
Asali: UGC

Hukumar zaɓe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben mazaɓar ta jihar Neja da kuri'u 47,942, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zaben NASS Ta Tsige Ƙarin 'Yan Majalisun Tarayya 2, Ta Ba APC da APGA Nasara

Da wannan ƙuri'u ya samu nasara kan babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Abdullahi Gbatamagi, wanda ya tashi da ƙuri'u 40,003.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma jam'iyyar APC da ɗan takararta, Mista Gbatamagi, sun garzaya Kotu, inda suka shigar da ƙarar domin ƙalubalantar nasarar Gana ta hannun lauyansu, Johnson Usman.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa zaben ba ingantacce bane domin an saɓa wa kundin dokokin zaben Najeriya 2022, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Sun kuma ƙara da cewa tazarar kuri'un da ke tsakani ba su kai adadin katunan zaɓe PVC da mutane suka karɓa a rumfunan zaɓen da ba a yi zaɓe ba ko kuma aka soke.

Wane Hukunci Kotun ta yanke?

Da yake yanke hukunci ranar Litinin, kwamitin alkalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Sylvester Godspower ya amince da hujjojin masu ƙara.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Sanatan PDP, Ta Bai Wa Ministan Tinubu a Jihar Arewa

Kotun ta soke ƙuri'un akwatuna 26 a mazaɓar, wanda hakan ya zabtare kuri'un da Gana ya samu zuwa 46,494 yayin da ƙuri'un ɗan takarar APC suka koma 39,159.

Wannan mataki na Kotu ya sa katin PVC da masu kaɗa kuri'a suka karba a akwatun da zaɓen da abun ya shafa suka zama 14,411.

Daga nan Kotun ta jingine takardar shaidar lashe zaben da INEC ta ba Gana, kana ta umarci a shirya zaɓe a rumfuna 26 da ta soke cikin wata 3 masu zuwa.

Abia: Kotu Ta Tsige 'Yan Majalisun Tarayya Biyu Na LP, Ta Ba APC da APGA Nasara

A wani rahoton na daban kuma Jam'iyyar Labour Party ta ƙara rasa kujerun 'yan majalisar wakilan tarayya a jihar Abia da ke Kudu maso Gabas.

Kotun sauraron ƙararrakin zaben NASS ta tsige 'yan majalisun guda biyu ranar Litinin, ta bayyana waɗanda suka ci zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262