Kwara: PDP Ta Nada Mataimakin Shugaban Jam'iyya, Sakatare da Wasu 2

Kwara: PDP Ta Nada Mataimakin Shugaban Jam'iyya, Sakatare da Wasu 2

  • Jam'iyyar PDP ta naɗa sabbin shugabanni guda huɗu a jihar Kwara bayan murabus din wasu a kwanakin baya
  • PDP ta naɗa mataimakin shugabanta na jiha, Sakatare, sakataren watsa labarai da kuma mukaddashin shugaban matasa
  • Wannan na zuwa ne bayan rigingimun da suka hana jam'iyyar zaman lafiya tun bayan babban zaɓen 2023

Jihar Kwara - Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kwara ta naɗa sabon mataimakin shugaban jam'iyya, Sakataren jam'iyya, Sakataren watsa labarai da muƙaddashin shugaban matasa.

Leadership ta ce PDP ta naɗa Alhaji Idris Mudashiru daga ƙaramar hukumar Baruten a matsayin mataimakin shugaban jam'iyya na jiha, da AbdulRahman Abdullahi Kayode a matsayin Sakatare.

Tutar jam'iyyar PDP.
Kwara: PDP Ta Nada Mataimakin Shugaban Jam'iyya, Sakatare da Wasu 2 Hoto: Leadership
Asali: UGC

Yayin da ta naɗa Olusegun Olusola Sholyment daga ƙaramar hukumar Isin a matsayin sakataren watsa labarai da Mallam Mohammed Abdulmunmini a matsayin muƙaddashin shugaban matasa.

Kara karanta wannan

Hadimai 2 Na Gwamnan PDP da Wasu Manyan Jiga-Jigai Sun Koma APC Ana Dab Da Sabon Zaɓe

Jam'iyyar ta yi wannan naɗe-naɗen ne bayan murabus din tsohon sakatare, Alhaji Rasaq Lawal, da sakataren watsa labarai, Prince Tunji Moronfoye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lawal da Moronfoye sun bayyana cewa sun ɗauki matakin yin murabus ɗin ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Haka nan kuma kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara, ya dakatar da shugaban matasan jam'iyya, Prince Haliru Dantsho, bisa zargin cin amana.

Jam'iyyar PDP zata fara gyara matsalolinta

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka ji shugaban PDP na jihar Kwara, Honorabul Babatunde Mohammed, yana cewa jam'iyyar na shirin kwaskwarima domin inganta ayyukanta.

Jam'iyyar PDP a Kwara na fama da rikicin cikin gida tun bayan babban zaɓen 2023 wanda ta sha ƙashi hannun jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Rigimar Jam'iyyar NNPP Ta Ɗauki Zafi, Kwankwaso Na Shirin Ɗaukar Muhimman Matakai Biyu

Ana hasashen cewa irin waɗan nan rigingimun na cikin gida da suka baibaye babbar jam'iyyar adawa na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo mata rashin nasara a zaben da ya gabata.

Hadimin Gwamna Diri da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar APC

A wani rahoton kuma Hadiman gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa 2 da wasu ƙusoshin siyasa sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ƙarshen mako.

Ɗan takarar mataimakin gwamnan APC a zaben Bayelsa da ke tafe, Joshua Maciver, shi ne ya tarbe su a gangamin ceto Sagbama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262