Wanda Suka Yi Aji Daya Da Shugaba Tinubu a Jami'ar Chicago Ya Yi Magana Kan Takardun Ƙaratunsa

Wanda Suka Yi Aji Daya Da Shugaba Tinubu a Jami'ar Chicago Ya Yi Magana Kan Takardun Ƙaratunsa

  • Mai sharhi kan al'amuran al'umma, Durojaiye Ogunsanya, ya yi magana kan batun cewa Shugaba Tinubu bai yi karatu a jami'ar jihar Chicago (CSU) ba
  • Ogunsanya ya bayyana cewa saɓanin iƙirarin da ƴan adawa ke yi, Shugaba Tinubu ya kammala karatunsa daga jami'ar CSU a Amurka
  • Mai sharhin ya bayyana cewa da shi da Shugaba Tinubu, ajinsu ɗaya a jami'ar kuma a tare suka kammala karatunsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Durojaiye Ogunsanya, wani mai sharhi kan al'amuran jama'a, ya bayyana cewa da shi da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ajinsu ɗaya a jami'ar jihar Chicago (CSU) ta ƙasar Amurka.

Ogunsanya, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talbijin na Television Continental, a ranar Litinin, 11 ga watan Satumban 2023.

Durojaiye ya yi magana kan karatun Tinubu a jami'ar jihar Chicago
Ogunsanya ya bayar da shaida cewa Tinubu ya yi karatu a jami'ar jihar Chicago Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa da shi da Shugaba Tinubu duk sun kammala karatunsu a jami'ar ne a shekarar 1979.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

"Tinubu ya halarci jami'ar jihar Chicago", tsohon ɗan ajinsu

Takardun karatun Shugaba Tinubu sun nuna cewa ya kammala karatunsa a jami'ar CSU a shekakar 1979 inda ya samu digiri a fannin harkokin kasuwanci, lissafin kuɗi da gudanarwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, akwai wasu ƴan zarge-zarge kan bambancin suna da ke a jikin takardun karatunsa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka yana neman a tilasta jami'ar Chicago ta saki bayanin karatun Tinubu.

Akwai ƴan Najeriya da dama waɗanda ba su yarda cewa Shugaba Tinubu ya kammala karatunsa a jami'ar ba. A taƙaice ma lauyoyin Atiku na cigaba ɗa ƙara ƙaimi kan ƙarar da suka shigar a Amurka.

Duk da hakan, Ogunsaya ga fito ya gaya wa duniya cewa lallai shugaban ƙasar ya yi karatu a jami'ar.

Kara karanta wannan

"Kowace Jiha 1,000" Shugaba Tinubu Ya Amince da Muhimmin Aiki a Jihohi 7 Na Arewacin Najeriya

A kalamansa:

"Tun da farko mutane fitina kawai su ke nema. Tare mu ka je jami'ar jihar Chicago. Ajin mu ɗaya a kwalejin kididdigar kuɗi da harkokin ƙasuwanci.
"Aji ɗaya mu ke tare da shi. Ya halarci jami'ar jihar Chicago kuma ya kammala ta.
"Na zo nan na bayar da shaida cewa ya halarci jami'ar sannan shi ɗalibi ne mai hazaƙa."

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a jihar Benue, ta tabbatar da nasarar sanatan Benue ta Kudu, Abba Moro na jam'iyyar PDP.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Daniel Onjeh ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da Moro ya samu a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng