Jam'iyyar APC Zata Yi Duk Mai Yiwuwa Domin Ta Ci Gaba da Mulkin Kogi, Ganduje
- Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar APC na ƙoƙarin sake samun nasara a zaben gwamnan jihar Kogi a watan Nuwamba
- Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban APC na ƙasa ya ce nasara ba zata yi wa jam'iyyar wahala ba saboda dama jihar a hannunta take
- Da yake jawabi a Sakkwato, Ganduje ya ce nasarorin gwamna Ahmed Aliyu ba a taba ganin irinsu ba cikin kwana 100
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kogi - Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da cewa jam'iyya mai mulki na aiki tuƙuru domin ta ci gaba da mulkin jihar Kogi.
Ganduje ya ba da wannan tabbacin ne yayin da zaɓen gwamnan jihar ke ƙara matsowa wanda zai gudana ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Ya ce jam’iyyar APC na yin duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da rike jihar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Da yake jawabi a jihar Sakkwato ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, 2023, Ganduje ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na san duk kunsan cewa jihar Kogi ta mu ce kuma tun ba yanzu ba muke samun nasara a jihar, saboda haka wannan karon lashe zaɓen ba zai mana wahala ba."
"Gwamnan mu ke jagorantar jihar kuma na san tunda muna da shi da ɗumbin nasararorin da ya samu zuwa yanzu, mun shirya tsaf domin shiga zaɓe."
Ganduje ya yaba wa gwamnan Sakkwato
Da yake tsokaci game da nasarorin da gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya cimma a kwanaki 100 na farko da hawa mulki, shugaban APC ya bayyana su a matsayin wadanda ba a taba ganin irinsu ba.
Sunnews ta rahoto Ganduje na cewa:
“Na zo kuma na ga nasarorin da Gwamna Ahmed Aliyu ya cimma wa kawo yanzu, kuma abin da na gani ya burge ni sosai."
“Gwamna matashi ne da ya shirya yin aikin. Ina ganin jim kaɗan bayan an ayyana shi a matsayin zababben gwamna, ya fara tsara abubuwan da zai yi da zaran ya shiga Ofis."
“Sakamakon shirinsa shi ne muke gani a yanzu. Lokacin da na zo nan, na shaida yadda ake raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa."
Allah Ne Ya Saka Mun Shiyasa Tinubu Ya Samu Nasara, In Ji Oyetola
A wani rahoton na daban kuma Tsohon gwamnan Osun kuma ministan Tinubu ya bayyana matsayarsa kan korar jiga-jigan tsagin Aregbesola daga APC.
Oyetola ya yi bayanin cewa yana goyon bayan matakin kora da dakatarwan da aka yi wa mambobin APC kana ya roƙi sauran masu kishin jam'iyya su yi aiki tukuru domin sake gina APC.
Asali: Legit.ng