Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP a Bayelsa, Ta Soke Zaben

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP a Bayelsa, Ta Soke Zaben

  • Kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Bayelsa ta yanke hukunci kan zaben mazabar tarayya ta Sagbama/Ekeremor
  • Kotun zaben ta yi watsi da nasarar Hon. Fred Agbedi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan ta soke zaben
  • Ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta sake sabon zabe cikin kwanaki 90

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bayelsa - Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, ta soke zaben mazabar tarayya ta Sagbama/Ekeremor sannan ta tsige Hon Fred Agbedi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kamar yadda AIT online ta rahoto, kwamitin kotun zaben ya umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar sahidar cin zabe da ta bai wa Agbedi nan take.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Abin da zai faru da PDP da LP idan sun tafi kotun koli – Gwamna Bello

Kotun zabe ta tsige dan majalisar tarayya na PDP a Bayelsa
Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP a Bayelsa, Ta Soke Zaben Hoto: Hon. Fredrick Yeitiemone Agbedi
Asali: Facebook

Hukuncin kotun zaben ya kuma umurci INEC da ta sake gudanar da sabon zabe cikin kwana casa'in ga masu zabe daa aka zalunta a zaben ‘yan majalisar dokokin jihar da ya gabata.

An tattaro cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne saboda tashe-tashen hankula da aka samu a lokacin zabe a mazabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, kotun zaben bata ayyana mai karan, Michael Olomu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben ba kamar yadda ya nema a cikin karar da ya shigar gaban kotu.

Kotu ta tabbatar da ratar kuri'a 9000 na Hon Agbedi

Kotun zaben ta ce tazarar kuri’u 9000 da Hon Agbedi ya samu a kan Olomu a zaben da ya gabata yana nan daram.

A cikin hukuncin, an umurci INEC da ta gudanar da sabon zabe a gudunmomi biyar da rumfuna sha daya da ke yankin Sagbama da kuma wasu gudunmomi na unguwa ta 11 da unguwa ta sha biyu a karamar hukumar Ekeremor wanda ke da masu rijista kimanin 26,000.

Kara karanta wannan

Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa N100, 000

Da yake martani kan hukuncin kotun, Hon Abedi ya bayyana cewa ba zai daukaka kara ba kuma a shirye yake ya tsaya takara a zaben da za a sake.

Kotun zabe ta tsige dan majalisar tarayya na LP a jihar Bayelsa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa kotun sauraron korafe-korafen zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Enugu ta yanke hukunci kan zaben mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo.

Kotun ta tsige dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo, Farfesa Sunday Nnamchi a inuwar jam'iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng