Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na LP, Ta Ayyana Dan PDP a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na LP, Ta Ayyana Dan PDP a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe

  • Kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisar tarayya ta sake tsige wani dan majalisar tarayya na jam’iyyar Labour Party a jihar Enugu, Farfesa Sunday Nnamchi
  • An soke zaben Nnamchi mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo a ranar Juma’a, 8 ga watan Satumba
  • Alkalan guda uku karkashin jagorancin A. M. Abubakar sun amince da cewa Nnamchi bai cancanci tsayawa takarar majalisar wakilai ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Enugu - Kotun sauraron korafe-korafen zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Enugu ta yanke hukunci kan zaben mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo.

Kotun ta tsige dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo, Farfesa Sunday Nnamchi a inuwar jam'iyyar Labour Party.

Kotun zabe ta kori Farfesa Sunday Nnamchi daga kujerar dan majalisar tarayya
Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na Labour Party, Ta Ayyana Dan PDP a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe Hoto: @ejykmykel1
Asali: Twitter

Farfesa Sunday Nnamchi bai cancanci tsayawa takara ba, kotun zabe

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, kwamitin mutum uku na kotun karkashin jagorancin Mai shari’a A. M. Abubakar, ta soke zaben Nnamchi sannan ta ayyana dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Prince Cornelius Nnaji, a matsayin zababben dan takara.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP a Bayelsa, Ta Soke Zaben

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar SaharaReporters, Nnaji, dan majalisar tarayya sau daya, ya kalubalanci nasarar Nnamchi a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Mai karar ya ce ba a dauki nauyin Nnamchi ba kuma bai cancanci tsayawa takarar kujerar dan majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar Labour Party ba.

Da take yanke hukunci, kotun zaben ta yarda cewar dan majalisar na LP bai cancanci tsayawa takarar zaben ba.

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Sanata APC, Ta Bai Wa Jam'iyyar PDP a Benue

A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya mai zama a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ta yanke hukunci kan zaben Sanatan Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Kotun ta ayyana Sanata Gabriel Suswam na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Abin da zai faru da PDP da LP idan sun tafi kotun koli – Gwamna Bello

Haka zalika Ƙotun ta tsige Sanata Emmanuel Udende na jam'iyyar APC daga kujerar mamba a majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Kotun zaɓen NASS da ke Makurɗi ta yanke hukunci ne a zamanta na yau Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023, wanda ya shafe sama da sa'o'i uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel