Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa Kudi

Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa Kudi

  • Kotun sauraron korafin zabe da ke Kano ta gagara rusa nasarar Sagir Koki (NNPP) a zaben 2023
  • Alkalai sun ce Lauyoyin Muntari Ishaq Yakasai ba su zo da hujjojin da za a soke hukuncin INEC ba
  • Kogi wanda yake Majalisar Tarayya ya samu N100, 000 a sakamakon karar da aka shigar a kan shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Kotun sauraron korafin zaben Majalisar Tarayya mai zama a garin Kano ya yi watsi da karar da aka shigar a kan Sagir Koki (NNPP).

Punch ta ce Muntari Ishaq Yakasai bai yi nasara a yunkurinsa na karbe kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya daga hannun Sagir Koki ba.

A hukuncin da Alkalan kotun uku su ka zartar a karkashin jagorancin Flora Azinge, an tabbatar da raunin hujjojin lauyan Muntari Yakassai.

'Yan NNPP a Kano
'Yan Majalisar NNPP a Kano Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Babu hujjar magudin NNPP

Kara karanta wannan

Sharrin Shari'a: Sanatocin APC da Kotu Ta Kora Kafin a Cinye Albashin Wata 3 a Majalisa

Mai shari’a Azinge ta ce wanda ya shigar da kara bai iya gamsar da kotu cewa an yi aringizo wajen kada kuri’a a rumfuna 25 a mazabarsa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun sauraron karar zaben ya ce hujjojin da mai kara ya gabatar gaban kotu ba su isa ba, kuma ba su da karfin da za a iya rusa zabe da su.

Wani rahoton da aka fitar ya ce alkalan sun ce shaidun je-ka-nayi-ka ‘dan takaran na APC ya gabatar, wadanda su ka dogara da an ce-ka ce.

Alkalan sun zargi lauyoyin Muntari Yakassai da gabatar da wasu takardun da ba su da alaka da shari’ar zaben ‘dan majalisar tarayyan da ake yi.

Kotu tayi kaca-kaca da hujjojin APC

A shaidar da su ka gabatar, masu bada shaidar sun tabbatar da ba su rumfar zaben a wuraren da su ka ce an yi aringizon kuri’a.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita

Ba su dace a yarda da maganarsu ba. Babu wani mai bada shaidan da za ayi imani da shi daga bayanan da su ka gabatar kai-tsaye.
Sannan ya gabatar da takardun da ba su da alaka domin nuna an saba doka, an yi aringizo, kuma ba a bi dokar zabe ta shekarar 2022 ba.
Saboda haka an bada N100, 000 ga wanda aka yi kara, an watsar da korafin saboda rashin shaida.

- Flora Azinge

Shari'ar zaben 2023 a kotu

Ku na da labari Natasha Akpoti-Uduaghan ta karbe wurin Sanata Abubakar Sadiku-Ohere kuma PDP ta yi galaba kan Sanata Thomas Onowakpo.

Kotun sauraron karar zaben ‘Dan majalisar Kogi ta gabas a 2023 ta raba Sanatan APC da kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng