Majalisar Dokokin Oyo Ta Amince Wa Gwamna Ya Karbo Bashin N50bn

Majalisar Dokokin Oyo Ta Amince Wa Gwamna Ya Karbo Bashin N50bn

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo zai karɓo bashin kuɗi Naira biliyan 50 domin gudanar da harkokin gwamnatinsa
  • Wannan ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi wa buƙatar a zamanta na ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023
  • Ya ce zai yi amfani da kuɗin wajen biyan albashi, tallafi da samar da kuɗaɗen kwangilolin da ake kan yi a Oyo

Jihar Oyo - Majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da buƙatar gwamnan jihar, Seyi Makinde, na runtumo bashin kuɗi kimanin Naira biliyan 50 domin tafiyar da harkokin gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar ta amince wa gwamnan ne biyo bayan wasiƙar da ya aika mata ta neman sahalewar 'yan majalisun kan ciyo bashin.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.
Majalisar Dokokin Oyo Ta Amince Wa Gwamna Ya Karbo Bashin N50bn Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dokokin, Honorabul Adebo Ogundoyin, shi ne karanta wasiƙar mai girma gwamna a zaman mambobi na ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamna Ya Janye Ƙarar da Ya Kai Gwamnan PDP Gaban Kotu, Bayanai Sun Fito

A wasiƙar, Gwamna Makinde ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan bukatar ta ciyo bashi wani bangare ne na kokarin gwamnati na samar da kudaden da take kashewa akai-akai wadanda suka hada da biyan albashi, tarurruka, da kuma kuɗin ci gaba da kwangiloli daban-daban."
"Rancen da zamu karɓo na tsawon watanni 45 ne da kuma ƙarin kashi 25% a kowace shekara."
"Sai dai wannan sharuɗɗa abu ne da za a iya sake dubawa da nazari dai-dai da yanayin musayar kudaɗe a kasuwa.

Majalisa ta amince da buƙatar Makinde

Bayan karanta wannan wasiƙa da muhawara kan buƙatar mai girma gwamnan, majalisar dokokin ta amince da runbumo wa al'ummar jihar Oyo bashin waɗan nan kuɗade, Vanguard ta rahoto.

Gwamna Makinde na jam'iyyar PDP na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka samu nasarar koma wa zango na biyu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Reshen Jihar Kano Ta Sanar Da Sabbin Matakan Da Ɗauka

Kuma yana cikin tawagar gwamnonin G-5 na jam'iyyar PDP karkashin jagorancin ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Tsohon Shugaban Jam'iyya Na Kasa, Rufa'i Ya Fice Daga NNPP

A wani rahoton mun kawo muku cewa tsohon shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufai Ahmed Alkali, ya fice daga jam'iyyar.

A wata sanarwa ranar Talata, Rufai ya bayyana cewa ya fahimci wannan rikicin da ya raba NNPP gida biyu ba mai ƙarewa bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262