Obasanjo: Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Ya Dauko Yar'Adu Duk da Na San Ba Shi Da Lafiya
- Olusegun Obasanjo ya bayyana gaskiyar yadda ya ɗauko Marigayi Yar'adua ya zama magajinsa duk da ya san ba shi da lafiya
- Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya ce zargin da ake jingina masa cewa ya san 'Yar'adua zai mutu shiyasa ya goya masa baya ba gaskiya bane
- Ya ce kwamiti ya kafa kuma suka tabbatar masa cewa Yar'adua mutum ne mai gaskiya, wanda ba zai saci kuɗin talakawa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana gaskiya cewa ya zabi marigayi Umaru Musa Yar’adua a matsayin magajinsa duk da ya san cewa ba shi da lafiya.
Obasanjo ya ce ya dauki matakin ne saboda shawarwarin da kwararrun likitoci suka bayar sun nuna cewa ‘Yar’adua, wanda aka yi masa dashen ƙoda, yana da lafiyar da zai iya aikin shugaban ƙasa.
"In Ka Isa Ka Ƙaryata" Shugaban NNPP Ya Tona Cin Amanar Da Kwnakwaso Ya Yi Kwana 4 Gabanin Zaɓen 2023
Daily Trust ta ruwaito cewa Obasanjo ya jagoranci Najeriya sau biyu; na farko a mulkin soja (1976-1979) sannan kuma a matsayin zababben shugaban ƙasa na farar hula (1999-2007).
Sai dai bayan kammala wa'adi biyu a 2007, mataimakin Obasanjo, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Ribas, Peter Odili, na cikin waɗanda suka nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a PDP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma Obasanjo ya zaɓi Umaru Musa 'Yar'adua, wanda Allah ya masa rasuwa lokacin yana kan mulki ranar 5 ga watan Mayu, 2010 daga wani abu da Likita ya kira, "Acute pericarditis."
Obasanjo ya bada labarin abinda ya faru
Da yake hira da jaridar The Cable, Obasanjo ya musanta zargin da ake masa cewa da gangan ya zaɓi ɗan takara mai rauni saboda son zuciyarsa.
Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya ce:
"Na kafa kwamiti bisa jagorancin Dakta Olusegun Agagu, domin zaƙulo wanda zai gaje ni. Sun yi mazari kan mutane da dama kuma sun gudanar da bincike mai zurfi a kansu, 'Yar'adua ne a sahun gaba."
"Sun kafa hujjar cewa mutum ne mai gaskiya kuma ba zai sace dukiyar al'umma ba. An tattauna batun rashin lafiyarsa kuma na miƙa rahoton ga kwararre domin ya bamu shawara."
"Bayan ya yi nazari kan rahoton Asibitin Umaru, ya ce alamu sun nuna an masa dashen ƙoda, kuma idan wannan ne kaɗai to babu wani abun damuwa domin zai samu lafiya kamar kowa."
"Wannan shi ne gaskiyar abinda ya faru, duk wani raɗe-raɗin cewa na san zai mutu shiyasa na mara masa baya ya zama shugaban ƙasa ba gaskiya bane."
Kungiyar NLC Ta Shure Gana Wa da Gwamnatinn Tarayya Kan Yajin Aiki
A wani labarin na daban Shugabannin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) sun ƙaurace wa halartar taron da Ministan Tinubu ya shirya a Abuja.
Ministan ya kira zaman ne da nufin shawo kansu su janye yajin aikin gargaɗi da suka shirya shiga a cikin makon nan.
Asali: Legit.ng