Yadda Shugaban Majalisa Ya Sakawa Mutanensa Da Mukamai Masu Tsoka

Yadda Shugaban Majalisa Ya Sakawa Mutanensa Da Mukamai Masu Tsoka

  • Tajudeen Abbas PhD ya samu galaba a zaben shugaban majalisar wakilai da aka yi da kimanin 99%
  • ‘Yan majalisa sun bada goyon bayansu ga ‘dan takaran jam’iyyar APC, su ka rabu da abokan adawarsa
  • Idris Wase, Aminu Jaji ba su samu wasu mukamai da ake ji da su ko shugabancin manyan kwamitoci ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Duk da jam'iyyar APC ta na da ‘yan majalisu 177, Abbas Tajuddeen ya samu kuri’u 353 a cikin 359, ya doke Idris Wase da Aminu Sani Jaji.

Wadanda ba su Abbas kuri’arsu ba su ne: Idris Wase, Aminu Jaji, Tijjani Ismail, Muhammed Abdulmummin, Ahmed Doro da Usman Bindawa.

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Idris Wase ya samu shugabancin kwamitin daidaiton mukamai a rabon da aka yi wannan karo.

Majalisa
'Yan Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kwana 100: Maryam Shetty da Wurare 5 da Tinubu Ya Canza Shawara Saboda Matsin Lamba

Jaji ya dawo da kafar hagu

Premium Times ta ce Jaji wanda ya ki yarda ya hakura da takarar shugabanci ya samu shugabancin kwamitin gidauniyar kula da muhalli ne.

Mutanen ‘dan majalisar ba su yi dace a rabon kwamitin da Rt. Hon.Abbas ya yi ba.

Ado Doguwa, Bichi sun yi dace

Alhassan Ado Doguwa ya na cikin shugabannin da za su kula da kwamitocin harkar man fetur, Yusuf Gagdi ya rike kwamitin harkar sojojin ruwa.

‘Dan majalisar APC daga Kano, Abubakar Bichi ya gaji Betara, haka Alhassan Rurum na NNPP daga Kano ya ga ladan goyon bayan 'dan takaran APC.

Sada Soli bai rasa shugabancin kwamitinsa na harkokin ruwa ba, amma an karbe kwamitin kasafi daga hannun Muktar Betara zuwa na birnin Abuja.

Sauran wadanda su ka nuna sha’awar kujerar; Abubakar Yalleman, Miriam Onuoha da Tunji Olawuyi duk sun samu shugabancin manyan kwamitoci.

Jagororin kamfe a Majalisa

Kara karanta wannan

Babu Mamaki Tinubu Ya Fatattaki Mutanen da Buhari Ya Ba Mukami Daf da Barin Mulki

Akin Alabi ya tsira da kujerar kwamitin ayyuka bayan zama kakakin kungiyar hadin-giwan da ta goyi bayan 'dan majalisar Zariya a zaben bana.

Kingsley Chinda da Bello Kumo sun taka rawar gani wajen doke Jaji da Wase, yanzu haka su na cikin shugabannin majalisa a matsayin sakayyarsu.

Sababbin shiga da ke da sa'a

Bamidele Salami, Jerry Alagbaso, da Nicholas Mutu ba su mara baya a banza ba yayin da jinkirin Wole Oke ya jawo ya rasa kujerarsa a majalisar kasar.

Bello El-Rufai, Ojutu Ejeme, Ikenga Ugochinyere da Regina Akume yanzu su ka zo majalisa amma sun ga amfanin goyon takarar Dr. Abbas da su ka yi.

Rikicinsu Kwankwaso a NNPP

Ku na da labari wasu 'yan tawaren jam'iyyar NNPP za su yi bincike a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan daya da aka samu wajen saida fam.

An yanke shawarar a gayyato hukumomin tsaro su yi binciken asusun jam’iyyar NNPP da kyau. Hakan zai jefa Rabiu Musa Kwankwaso a matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng