Jam'iyyar APC Zata Buɗe Ofisoshi a Gundumomi 8,813 a Najeriya, In Ji Ganduje

Jam'iyyar APC Zata Buɗe Ofisoshi a Gundumomi 8,813 a Najeriya, In Ji Ganduje

  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana sabon shirinsa na matso da jam'iyyar APC kusa da 'yan Najeriya
  • Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya ayyana shirinsa na gina ofisoshin jam'iyyar a duka gundumomi sama da 8,000 da ke faɗin ƙasar nan
  • Tsohon gwamnan ya roki ɗaukacin mambobin APC da su mara wa ɗan takarar gwamna, Ododo baya a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kogi - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na gina ofisoshin jam'iyyar a duka gundumomi 8,813 da ke faɗin Najeriya.

Ganduje ya ce zai yi wannan aiki ne domin ƙara matsar da jam'iyya mai mulki kusa da al'umma, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar APC Zata Buɗe Ofisoshi a Gundumomi 8,813 a Najeriya, In Ji Ganduje Hoto: Sen. Ohere Sadiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Kano ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC ta kai matakin ƙarshe a shirye-shiryen gina cibiyar nazarin ci gaba ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Ganduje Ya Hango Romo a Jihar PDP, Ya Ce Nan Kusa Zai Kwace Ya Ba APC

Dakta Ganduje ya faɗi haka ne ranar Asabar a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a wurin taron kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaben APC a zaben gwamna mai zuwa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zamu lashe zaben gwamnan Kogi - Ganduje

Ganduje ya yi kira ga daukacin mambobin APC da masu ruwa da tsaki da su hada kai da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Alhaji Ododo Ahmed, domin samun nasara a zabe mai zuwa.

A cewarsa, jam’iyya mai mulki ta yi imanin cewa za a iya ɗaukar taken 'ci gaba' a matsayin akidar siyasa domin inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya.

A rahoton jaridar Sunnnews, shugaban APC Ganduje ya ce:

“Don haka ina kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyarmu da masu ruwa da tsaki da su hada kai da ɗan takararmu na gwamna domin jam’iyyar mu ta samu nasara."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fusata Kan Matsalar Tsaro, Zai Fallasa Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin 'Yan Ta'adda

"Idan muka yi haka, duk ayyukan da aka bari za su ɗore kuma zamu ci gaba da gudanar da mulki a jihar Kogi."
"A jam’iyyar mu ta APC, mun himmatu wajen yin aiki tukuru a daidaiku da kuma dunƙule wuri ɗaya ba don komai sai domin cimma kyawawan manufofi da kudirorin mu."

Tsohon gwamnan na Kano, ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya da su ƙara hakuri su ci gaba da marawa shugaba Bola Tinubu baya a kokarinsa na magance matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.

Obaseki Vs Shaibu: Gwamnatin Edo Ya Sauya Wa Mataimakin Gwamna Ofis

A wani rahoton na daban Rikici tsakanin gwamna da mataimakinsa ya kara tsananta a jihar Edo yayin da gwamnati ke shirin sauya wa Shaibu ofis.

Ga dukkan alamu gwamnatin Obaseki na shirin fitar da mataimakin gwamna daga gidan gwamnati zuwa wani wuri daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262