Obaseki Vs Shaibu: Gwamnatin Edo Ya Sauya Wa Mataimakin Gwamna Ofis
- Rikici tsakanin gwamna da mataimakinsa ya kara tsananta a jihar Edo, gwamnati ta sauya wa Shaibu ofis
- Ga dukkan alamu gwamnatin Obaseki na shirin fitar da mataimakin gwamna daga gidan gwamnati zuwa wani wuri daban
- A halin yanzun alaƙa ta yi tsami tsakanin gwamna Godwin Obaseki da Philip Shaibu dukkansu 'ya'yan jam'iyyar PDP
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Edo - Biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin gwamnan Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, gwamnatin jihar ta fitar da ofishin mataimakin gwamnan daga gidan gwamnati.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sabon ofishin mataimakin gwamnan yana lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, kusa da gidan gwamnatin jihar Edo.
Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci wurin, ya lura da cewa an sanya wani allo mai dauke da rubutun, “Ofishin Mataimakin Gwamna” wanda aka kafa a kofar shiga ginin.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan da ke aiki a wurin ya bayyana cewa suna tsammanin kammala ginin daga nan zuwa ranar Litinin mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce bai san me za a yi da ginin ba, inda ya kara da cewa ko kaɗan bai ga allon sanarwan da aka sanya a kofar shiga ba, kamar yadda Dailypost ta rahoto.
Gwamnati da yi magana kan batun
Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama'a, Chris Nehikhare, ya ce, "Idan har akwai allon da gwamnatin ta kafa a hukumance, to hakan ne."
Dambarwar neman gaje kujarar gwamnan ce ta haddasa zaman doya da manja tsakanin Shaibu da mai gidansa, lamba ɗaya a jihar Edo.
Shaibu, wanda ya fito daga yankin Edo ta Arewa, yana da niyyar ya gaji Obaseki, ɗan asalin Benin a yankin Edo ta Kudu, amma gwamnan ya fi son wanda zai gaje shi ya fito daga ƙasar Esan a yankin Edo ta tsakiya.
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda mataimakin gwamnan ya fice daga wurin wani taro da gwamnatin jihar ta shirya bayan jami'an tsaro sun hana muƙarrabansa shiga.
Lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka hana Shaibu damar ganawa da Gwamna Godwin Obaseki, ranar Lahadi.
Muna da Kananan Yara 500,000 Da Ba Su Zuwa Makaranta a Kaduna, In Ji Uba Sani
A wani rahoton na daban Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa adadin yara 500,000 ne ba su zuwa makaranta a Kaduna.
Malam Sani ya faɗi haka ne a taron gaddamar da fara ginin sabbinNmakarantun sakandire 62 a faɗin kananan hukumomi 23.
Asali: Legit.ng