Iyorchia Ayu Zai Koma Matsayinsa Na Shugaban PDP Na Ƙasa? Kotu Ta Yanke Hukunci

Iyorchia Ayu Zai Koma Matsayinsa Na Shugaban PDP Na Ƙasa? Kotu Ta Yanke Hukunci

  • Babbar kotun jihar Benuwai mai zama a Gboko ta yanke hukunci kan ƙarar da ta nemi a maida Iyorchia Ayu a matsayin shugaban PDP
  • Mai shari'a D. M Igyuse, ya yi fatali da ƙarar wacce ta nemi Kotu ta jingine dakatarwan da aka yi wa Ayu a gundumarsa
  • Lokacin da yake sanar da hukunci kan ƙarar, Alkalin ya ayyana ƙarar da mafi munin cin mutuncin shari'a

Benue - Babbar Kotun jihar Benuwai mai zama a Gboko ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar gabanta mai neman ta maida Iyorchia Ayu muƙaminsa na shugaban jam'iyyar PDP ta ƙasa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Alkalin Kotun, mai shari'a D. M Igyuse, ya kori ƙarar, inda ya bayyana ta da cin mutuncin matakan shari'a.

Tsohon shugaban PDP na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu.
Iyorchia Ayu Zai Koma Matsayinsa Na Shugaban PDP Na Ƙasa? Kotu Ta Yanke Hukunci Hoto: @Iyorchiaayu
Asali: UGC

Wane hukunci Kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Bayan Juyin Mulkin Gabon, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ainihin Abinda Yake Jin Tsoron Ya Faru

Alƙalin ne ya bayyana haka yayin da yake karanto hukuncin da Kotu ta yanke ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, 2023, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun da farko, wani mai suna Nongo Ordue ne ya shigar da ƙarar gaban Kotun a madadin shugabanni 17 na gundumar Igyorov, ƙaramar hukumar Gboko, inda Ayu ya fito.

Ya roƙi Kotu ta soke dakatarwan da aka yi wa Sanata Ayu daga PDP a gundumar kana ta maida shi kujrarsa ta shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.

Amma lauyan PDP, Clement Mue, ya yi musun cewa ƙarar cin mutuncin shari'a ne saboda tuni babbar Kotu mai zama a Makurɗi ta yanke hukunci kan batun a ƙara mai lamba MHC/85/2023.

A hukuncin Kotun, ta yanke cewa Ayu ba zai sake koma wa kujarar shugaban jam'iyyar PDP ba sakamakon rasa katin zama mamba a gundumarsa.

Kara karanta wannan

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban Jam'iyya Ya Faɗi Wanda Yake da Tabbacin Zai Samu Nasara a Kotu

Ƙarar ta saɓa wa matakan shari'a a Kotu

Alkalin Kotun ya bayyana cewa wanda ke ƙara ya shigar da irinta a babbar Kotu ta 3 mai zama a Gboko mai lamba, GHC/36/2023, kuma aka yi watsi da ita ranar 27 ga watan Yuni.

Saboda haka mai shari'a Igyuse ya kori ƙarar kuma ya bayyana ta da, "Mafi munin cin mutuncin matakan shari'a."

Matakan Shugaba Tinubu Sun Fara Dawo da Zaman Lafiya a Zamfara,.Inji Yari

A wani labarin na daban Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'azizi Yari ya ce kyawawan ayyukan Tinubu sun fara dawo da zaman lafiya a jihar

Yari, Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma ya ce haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba yana da alaƙa da rashin tsaron da ake fama da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262