Bayelsa: Kodinetan Yakin Neman Zaben Peter Obi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

Bayelsa: Kodinetan Yakin Neman Zaben Peter Obi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Yayin da ake tunkarar zaben gwamna a jihar Bayelsa, babban jigon LP ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
  • Mista Alagoa Morris, Ko'dinetan kamfen Peter Obi, ya ce gwamna Diri ya yi abinda ya dace a Bayelsa don haka shi zai goyi baya
  • A cewarsa, da yawan mutane ba su san wasu ayyukan da gwamna mai ci ya yi ba amma yana matuƙar kokari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bayelsa - Kodinetan kwamitin yaƙin nemaan zaɓen Peter Obi (PCC), Mista Alagoa Morris, ya sauya sheka daga jam'iyyar Labour Party (LP) zuwa jam'iyyar PDP.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Mista Morris, ɗan gwagwarmayar kare muhalli, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta, 2023 a Yenagoa, babban birnin jihar.

Jigon LP ya sauya sheka zuwa PDP a Bayelsa.
Bayelsa: Kodinetan Yakin Neman Zaben Peter Obi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: thenation
Asali: Facebook

Babban jigon LP ya koma jam'iyyar PDP ne yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Bayelsa wanda aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Ganduje Na Yiwa APC Wankan Tsarki, An Kori Na Hannun Daman Tsohon Minista Aregbesola Su 84

A jawabinsa, ya ce gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP ya zuba ayyuka masu kyau, wasu daga cikinsu ba bu wanda ya sani, shiyasa ya ga dacewar ya mara masa baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwayar Daily Post, Mista Morris ya ce:

"Na yanke shawarar goyon bayan tazarcen gwamna mai ci saboda ya fi dukkan manyan 'yan takarar cancanta da nagarta."
"Idan ka duba 'yan takarar da muke da su waɗanda zasu fafata a zaben gwamna ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, gwamna Diri ne kaɗai ya cancanci mu mara masa baya."
"Ni ba mamban jam’iyyar LP ba ne kafin su nada ni a matsayin ko’odinetan kamfe na jiha, kuma wannan aikin da suka bani ya kammala, don haka zamu ci gaba da wasu harkokin."

Gwamna Diri muke buƙata ya ci gaba - Morris

Bugu da ƙari, jigon siyasar ya bayyana cewa ya gana da gwamna Diri kuma yana da yaƙinin cewa shi ne mutum ɗaya tilo da ya cancanta mutane su zaɓa a zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami

“Diri ya yi abubuwa da yawa da jama’a ba su sani ba, ina ganin ya yi kokari, don haka dole ne mu ba shi goyon baya domin ya ci gaba,” inji shi.

Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Kori CMD Na Asibitin Hasiya Bayero

A wani labarin kuma Gwamnatin jihar Kano ta kori shugaban Asibitin yara Hasiya Bayero, Dakta Yunusa Sanusi, saboda rashin iya jagoranci.

Hukumar kula da Asibitoci ta jihar (HMB) ta ce an ɗauki wannan matakin ne bayan dogoron nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262