Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Gudanarwa Na Hukumar NDDC

Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Gudanarwa Na Hukumar NDDC

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin sabbin muƙamai a gwamnatinsa
  • Shugaban ya naɗa sabbin shugabannin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja Delta
  • Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rantsar da sabbin ministocin da Shugaba Tinubu ya yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabon kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya naɗa shugabannin gudanarwa na NDDC
Tinubu ya sanar da naɗin sabbin shugabannin gudanarwa na hukumar NDDC. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugabannin gudanarwa na NDDC da Tinubu ya naɗa

Sabbin shugabannin gudanarwa na kwamitin Neja Delta da Shugaba Tinubu ya naɗa sun ƙunshi:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

To Fa: Ciyaman Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Gwamnan APC Ke Turmushe Kuɗin Kananan Hukumomi

Mr. Chiedu Ebie – Shugaba daga jihar Delta

Dr. Samuel Ogbuku – Manajan darakta daga jihar Bayelsa

Mr. Boma Iyaye – Babban daraktan harkokin kuɗi daga jihar Rivers

Mr. Victor Antai – Babban daraktan aikace-aikace daga jihar Akwa-Ibom

Ifedayo Abegunde – Babban daraktan gudanarwa daga jihar Ondo

Ƙarin mambobin hukumar sun haɗa da: Sanata Dimaro Denyanbofa daga Bayelsa, Mista Abasi Ndikan Nkono daga jihar Akwa Ibo, Honarabul Monday Igbuya daga Delta, Tony Okocha daga Rivers, Honarabul Patrick Aisowieren daga Edo da kuma Mista Kyrian Uchegbu daga jihar Imo.

Sauran mambobin su ne, Victor Kolade Akinjo daga Ondo, Dimgba Eruba daga Abia, Mr. Asu Oku Okang daga Cross River, Honarabul Nick Wende - wakilin Arewa ta Tsakiya, Honarabul Namdas Abdulrazak - wakilinin Arewa maso Gabas, da kuma Dakta Ibrahim Abdullahi Gobir – wakilin Arewa maso Yamma.

Tinubu zai rage yawan masu zuwa taron majalisar dinkin duniya

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawa a baya, Shugaba Tinubu ba da umarnin hana biza ga wasu daga cikin muƙarrabansa da ke son zuwa taron majalisar ɗinkin duniya ba tare da dalili ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

Kakakin Bola Tinubu, cif Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan, inda ya ce shugaban ya ɗauki matakin ne domin rage yawan kuɗaɗen da za a kashe daga lalitar gwamnati.

Shugaban ya buƙaci a hana duk wanda ba shi cikin lissafin bizar zuwa wajen taron, wanda za a yi a Amurka kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Tinubu zai biya mazauna Abuja diyyar N825.8b na gidajensu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan alƙawarin da gwamnatin Tinubu ta yi na bai wa mazauna birnin tarayya Abuja diyyar N825.8b saboda gidajen su da za a taɓa.

Ministan birnin tarayyar Nyesom Wike ne ya bayyana hakan, inda ya ce an ware kuɗaɗen ne domin biyan mazauna Abuja da za su rasa muhallansu saboda aikin titin jirgi da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng