Phillip Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Fice Daga Dakin Taro Bayan Hana Hadimansa Shiga
- Phillip Shaibu ya jagoranci muƙarrabansa sun bar wurin taron da gwamnatin jihar Edo ta shirya ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023
- Mataimakin gwamnan ya bar wurin ne bayan kunyata shi da jami'an tsaro suka yi tun a ƙofar shiga ɗakin da aka shirya taron
- A wani faifan bidiyo da aka yaɗa, an ga mataimakin gwamnan na rokon a bar tawagarsa ta shiga wurin amma abu ya ci tura
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Edo state - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Phillip Shaibu, ya fice daga ɗaƙin taron da ya halarta ranar Litinin a jihar bayan an hana hadimansa da dogaransa shiga wurin.
A wani faifan bidiyo da kafar talabijin ta Arise ta wallafa ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023, an bar mataimakin gwamnan ya shiga wurin taron bikin cika shekaru 60 da gwamnatin jihar ta shirya.
Sai dai abin mamakin, yayin da hadimansa da kuma jami'an tsaron da ke ba shi kariya suka yi yunkurin shiga wurin, nan take aka hana su shiga.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa duk da Mista Shaiba ya nemi izinin a bai wa hadimansa dama su shiga wurin taron, an ga jami'an tsaro sun toshe hanyar sun hana su shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan wani ɗan lokaci da ya yi kama da jiran ganin abinda zai faru, mataimakin gwamnan ya yi wa tawagarsa alamar su bar wurin, inda aka ji ya ce, "Mu tafi."
An ga mataimakin gwamna wanda alamu suka nuna ƙarara bai ji daɗin abinda ya faru ba, ya jagoranci mukarrabansa suka fito daga wurin kana suka hau motocinsu suka ƙara gaba.
Yadda ake zaman doya da manja
A ‘yan makonnin da suka gabata, Godwin Obaseki, gwamnan Edo da Shaibu sun yi takun-saka kan batutuwan da suka shafi shirin tsige mataimakin gwamnan.
A cikin watan Yuli, Shaibu ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja domin ta hana wannan shiri na tsige shi.
Sai dai Obaseki da Blessing Agbebaku, kakakin majalisar dokokin Edo, sun musanta shirin tsigewar da ya ke zargi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Gwamnatin Tinubu Zata Ɗauki Sabbin Ma'aikata 300,000
A wani rahoton na daban Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin ma'aikata 300,000 a sabuwar hukumar dakile yaɗuwar makamai (NATCOM).
Muƙaddashin shugaban hukumar, Otunba Adejare Rewane, ya ce za a ɗauki mutane 7,000 a kowace jiha da kuma Abuja.
Asali: Legit.ng