Hadimin Atiku Ya Fadi Lokacin Da Za a Tsige Tinubu Daga Kan Kujerarsa, Ya Ba Shi Muhimmiyar Shawara
- Daniel Bwala, tsohon hadimin Atiku Abubakar na yaƙin neman zaɓe, ya ce Tinubu na shugabanci ne na wucin gadi
- Bwala ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Atiku Abubakar zai ƙwace kujerar Tinubu a Kotu
- Tsohon kakakin na Atiku ya bayyana hakan ne a cikin sharhi da ya yi kan wani rubutu da aka wallafa a manhajar X
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon hadimin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya ce watanni biyu ne suka ragewa jam'iyyar APC ta bar Villa.
Bwala ya bayyana hakan ne a yayin da yake sharhi kan wani rubutu da aka wallafa a shafin X (Twitter a da).
Bwala ya ba Tinubu shawara kafin kotu ta sauke shi
A bisa dalilin na Bwala ne ya shawarci Tinubu ya naɗa Femi Fani-Kayode a matsayin minista gabanin mai gidansa ya amshe kujerar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fani-Kayode tsohon mai ba da shawara ne a lokacin Obasanjo, daga 2003 zuwa 2006, haka nan ya riƙe muƙamin minista har sau biyu a shekarun baya.
Sai dai duk da jajircewarsa a lokacin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu, Femi Fani-Kayode bai samu shiga cikin sama da ministoci 40 da aka naɗa ba.
Atiku ya ce babu Firamare da Sakandare a bayanan karatun Tinubu
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan iƙirarin da tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi na cewa babu Firamare da Sakandare a bayanan karatun Tinubu.
Atiku ya ce wannan wani abu ne da ya kamata ace 'yan Najeriya sun nuna matuƙar damuwarsu a kansa ba wai su kawar da kai ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, (wato Twitter a da).
Jami'ar Chicago ta amince za ta saki takardun karatun Tinubu
Legit.ng a wani labarin mai alaƙa da wannan ta yi rahoto kan bayanin da jami'ar jihar Chicago ta ƙasar Amurka ta yi na cewa za ta saki bayanin karatun Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai jami'ar ta ce ba za ta saki takardun ga kotu ba har sai ta gama nazari kan abinda ke tsakanin Atiku da Tinubu.
Asali: Legit.ng