Atiku Ya Samo Makamar Kwace Mulkin Tinubu, Ya Gano Tsaiko a Bayanan Shugaban Kasar Na 1999 da 2023

Atiku Ya Samo Makamar Kwace Mulkin Tinubu, Ya Gano Tsaiko a Bayanan Shugaban Kasar Na 1999 da 2023

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, ya yi zargin cewa bayanan karatun shugaban kasa Tinubu bai nuna karatunsa na firamare da sakandare ba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ikirarin ya yi karo da bayanan Tinubu na 1999 lokacin da ya yi takarar gwamnan jihar Lagas
  • A cewar Atiku, bayanan karatun Tinubu abun damuwa ne, cewa ta yaya zai je jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka ba tare da karatun firamare da sakandare ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya zargi Shugaban kasa Bola Tinubu da kauracewa karatun fimare da sakandare don komawa jami’ar jihar Chicago.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, a wani rubutu da ya yi a manhajar X a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, ya ce ya kamata ikirarin Tinubu a 2023 ya zama abun damuwa ga daukacin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jigon APC Ya Yi Hasashen Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke

Atiku ya dasa ayar tambaya kan yadda aka yi shugaban kasar ya halarci jami’ar jihar Chicago a kasar Amurka ba tare da karatun firamare da sakandare ba a Najeriya.

Atiku bai gamsu da bayanan karatun Tinubu ba
Atiku ya samo makamar kwace mulkin Tinubu, ya gano tsaiko a bayanan Tinubu na 1999 da 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Yadda bayanin karatun Tinubu ya yi karo da bayanansa na 1999

A cewar jigon na PDP, Shugaban kasa Tinubu a 1999, ya yi ikirarin cewa ya halarci:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Makarantar Firamare na St. John, Aroloya, Lagas kafin ya tafi makarantar Children's Home a Ibadan. Ya ce wuri na gaba da ya je yawon karatu shine kwalejin gwamnati na Ibadan, Richard Daley College da jami’ar jihar Chicago a kasar Amurka."

Atiku ya kuma yi zargin cewa bayanan karatun shugaban kasa Tinubu a 2023 ya sha banban da abun da ya gabatar a 1999, yana mai cewa shugaban kasar ya dai ce kawai ya halarci jami'ar jihar Chicago ba tare da karatun firamare da sakandare ba.

Kara karanta wannan

Mukamin Minista: Dalilin Da Yasa Shugaban Kasa Tinubu Ya Ajiye Kwankwaso, Majiyoyi Sun Bayyana

Kuma dai, Atiku ya sake dasa ayar tambaya a bayanan karatun Tinubu

Daga nan sai tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna mamakinsa game da abun da aka gano. Ya tambaya:

"Abun mamaki, a 2023 Tinubu ya tsaya kan cewa ya halarci @ChicagoState kawai. Ina susa kaina. Ta yaya hakan zai yiwu?"

Shugaban kasa Tinubu ya kayar da Atiku a zaben shugaban kasa na 2023. Duk da haka, ya kalubalanci sakamakon zaben a kotun zaben shugaban kasa, yana mai dasa ayoyin tambaya da dama kame da karatun shugaban kasar.

Bai Kamata Jami'ar Chicago Su Bayyana Takardu Na Ga Atiku Ba, Tinubu

A gefe guda, mun ji a aya cewa shugaba Bola Tinubu ya fadi dalilan da yasa bai kamata kotun Amurka ta saki takardun karatunsa ba na jami’ar Chicago.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani game da karar tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shigar na bukatar shaidar karatun Tinubu daga jami’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng