Tinubu vs Atiku: Jigon APC Ya Yi Magana Kan Yadda Hukuncin Kotu Zai Kaya
- Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi magana kan ƙarar da Atiku Abubakar ya ke yi wa Shugaba Tinubu a Amurka
- A halin da ake ciki, jami'ar jihar Chicago, ta bayyana cewa za ta saki takardun karatun Shugaba Tinubu idan kotu ta bayar da umarni
- Da yake martani, Aaron Artimas, kakakin jam'iyyar APC a jihar Taraba, ya bayyana cewa ƙarar ta Atiku a kan Shugaba Tinubu ba za ta taka rawa ba wajen hukuncin da za a yanke a Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jalingo, jihar Taraba - Aaron Artimas, kakakin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa ƙarar da Atiku Abubakar ya ke yi a kan Shugaba Tinubu a kotun Amurka, ba ta da wani muhimmanci kan hukuncin da za a yanke a kotun zaɓen shugaban ƙasa.
Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Sabbin Bayanai Kan Matsayar ECOWAS
A cikin ƴan kwanakin nan, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a kotun Illinois a Chicago, ƙasar Amurka, domin neman tilasta jami'ar jihar Chicago ta saki takardun karatun Shugaba Tinubu.
Da yake martaninsa, Mr. Artimas a wata hira da Legit.ng a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ƙarar ta Atiku babu wata rawa da za ta taka wajen hukuncin da za a yanke a shari'ar zaɓen shugaban ƙasa.
Kakakin ya bayyana ƙarar ta Atiku a matsayin abin mamaki, inda ya ƙara da cewa ba ta da wani amfani ta fuskar shari'a.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mr. Artimas ya bayyana cewa:
"Ƙarar Atiku Abubakar abin mamaki ce kawai sannan babu wata rawa da za ta taka a kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa. Lokaci ya ƙure masa."
Atiku vs Tinubu: "maganar karatu ce kawai" inji kakakin APC
Kakakin na jam'iyyar APC ya nuna kuskuren ƙarar ta Atiku a kan Shugaba Tinubu. A cewarsa tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana da babban aiki a gabansa a ƙoƙarin da ya ke yi na ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.
Mr. Artimas ya yi nuni da cewa ƙarar ta Atiku magana ce kawai ta karatu domin sanya mutane su yi alamar tambaya a kan mutuncin Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Matsayar ECOWAS
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinuɓu ya bayyana matsayar ECOWAS kan rikicin Jamhuriyar Nijar.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa yaƙi ba abun so bane amma dole ne a kare dimokuraɗiyya a ƙasar.
Asali: Legit.ng