Shehu Sani Ya Ce Wasu Tsoffin Gwamnoni Da Ke Gwamnatin Tinubu Karin Nauyi Ne a Gareshi

Shehu Sani Ya Ce Wasu Tsoffin Gwamnoni Da Ke Gwamnatin Tinubu Karin Nauyi Ne a Gareshi

  • Tsohon sanatan Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan salon mulkin Tinubu
  • Ya ce idan Tinubu ya yi da kyau, jama'a za su yabe shi, akasin haka kuma su caccake shi
  • Sai dai Shehu Sani ya bayyana cewa wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da ya ba muƙamai, ƙarin nauyi ne ga gwamnatinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci kan muƙaman ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya raba a makon da ya gabata.

Ya ce wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da Tinubu ya bai wa muƙamin minista ba komai ba ne illa ƙarin nauyi ga gwamnatinsa.

Shehu Sani ya ce tsoffin gwamnoni ne suka kewaye Tinubu
Shehu Sani ya ce tsoffin gwamnonin da Tinubu ya naɗa ministoci ƙarin nauyi ne a gareshi. Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shehu ya ce tsoffin gwamnoni sun kewaye Tinubu

Shehu Sani a zantawarsa da jaridar The Punch, ya ce tun bayan hawan Bola Tinubu mulki 'yan Najeriya suke dakon ganin ya zaɓo jajirtattun mutane a matsayin ministocin da zai yi aiki da su.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnatin Tinubu Zata Rage Farashin Siminta a Najeriya, Minista Ya Magantu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai Sani ya bayyana cewa wasu tsoffin gwamnoni da suke ganin cewa dole ne Tinubu ya ba su muƙami saboda gudummawar da suka ba shi ne suka kewaye shi.

Ya ƙara da cewa mafi yawa daga cikinsu tsoffin gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya ne da suke ganin sun taka rawa wajen tabbatar da cewa shugabanci ya koma kudu.

Shehu ya kuma ce muddun sun yi hakan ne don samun daidaito ba don muƙami ba, kamata ya yi su miƙa sunayen wasu da suka fi su cancanta daga jihohinsu.

Shehu Sani ya yaba da naɗin wasu ministocin na Tinubu

Sai dai tsohon sanatan ya yaba da naɗin wasu daga cikin ministocin na Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce ministan lafiya, ministan harkokin waje da kuma na tattalin arziƙi duk sun cancanta saboda gogewarsu da kuma sanin makamar aiki kamar yadda suka yi aka gani a baya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Gwamnonin APC Ko Na PDP Da Ya Kamata Yan Najeriya Sun Canja

Shehu ya ce tsoffin gwamnonin da Tinubu ya naɗa kuwa ba komai ba ne sai ƙarin nauyi, musamman ma da ya zamto cewa mafi yawansu sun sace dukiyoyin jihohinsu a lokacin da suke kan madafun iko.

An bayyana dalilin da ya hana Tinubu nada Kwankwaso minista

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu bai naɗa Kwankwaso a matsayin ɗaya daga cikin ministocinsa ba.

Gabanin fitar da sunayen mutane 48 da Tinubu zai yi aiki tare da su a matsayin ministoci, labarai sun bazu cewa Rabiu Musa Kwankwaso na cikin waɗanda za a naɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng