Rikicin APC: Ganduje Ya Rantsar Da Sabbin Mambobin NWC Da Tsakar Dare
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin mambobin kwamitin NWC
- Jam'iyya mai mulki ta rantsar da kwamitin ne yayin da wasu manyan masu ruwa da tsaki suka yi zanga-zanga kan wadanda aka zaba
- An rantsar da mambobin su shida a tsakar daren ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta, a sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke Abuja
Abuja - Daga karshe jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) guda shida yayin da ake tsaka da gagarumin zanga-zanga.
An rantsar da su ne a sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke babban birnin tarayya Abuja a tsakar daren ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta, saboda zanga-zangar da aka yi kan zaben sabbin mambobin, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Jerin mambobin kwamitin NWC na APC da aka rantsar
Vanguard ta rahoto cewa sabbin mambobin da shugaban jam'iyyar na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya rantsar sune mataimakin shugaban jam'iyyar (arewa), Hon. Ali Bukar Dalori; Hon. Garba Datti Muhammad (mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, arewa maso yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai Farfesa Abdul Karim Abubakar Kana (Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a na kasa); Hon. Donatus Nwankpa (Sakataren walwala na jam'iyyar na kasa); Mary Alile Idele (Shugabar matar jam'iyya na kasa) da Duro Meseko (Mataimakin sakataren labaran jam'iyya na kasa).
Yadda rikici ya kunno kai a APC kan zaben mambobin kwmaitin NWC
Ku tuna cewa an shirya rantsar da su ne a ranar Alhamis amma sai masu zanga-zanga karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello da sauran mutane daga Cross River suka kawo tsaiko ga shirin rantsarwar.
A safiyar ranar Juma'a, masu ruwa da tsaki na APC a Abia da manyan jam'iyya sun yi watsi da tsarin da ya kai ga zabar Donatus Nwankpa a matsayin madadin marigayi Friday Nwosu a matsayin sakataren walwala na jam'iyyar kuma wakilin Abia a kwamitin NWC.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Bello, da yan majlisun tarayya na jihar Kogi sun ziyarci babbar sakatariyar APC ta kasa bayan an yi watsi da sunan da suka aiko.
Haka zalika a ranar Laraba, ministar jin kai da yaye talauci, Betta Edo, ta ziyarci hedkwatar APC kan sabuwar shugaban mata da aka nada maimakon wacce ta turo.
Dalilin da yasa Tinubu bai bai wa Kwankwaso minista ba
A wani labari na daban, mun ji cewa akwai alamu masu karfi da suka nuna cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin daya daga cikin ministocinsa.
Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban Kwankwasiyyar sau biyu, wanda daga baya shima ya tabbatar da cewar suna tattaunawa kan yiwuwar yin aiki tare da shugaban kasar.
Sai dai kuma, ga mamakin mutane da dama, Kwankwaso bai samu shiga jerin ministocin 48 da shugaban kasar ya saki ba.
Asali: Legit.ng