Mukamin Minista: Dalilin Da Yasa Shugaban Kasa Tinubu Ya Ajiye Kwankwaso, Majiyoyi Sun Bayyana

Mukamin Minista: Dalilin Da Yasa Shugaban Kasa Tinubu Ya Ajiye Kwankwaso, Majiyoyi Sun Bayyana

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya so nada Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP, a matsayin minista
  • An yi wa yunkurin kallo a matsayin wata dabarar Tinubu na samun goyon bayan Kwankwaso da kuma yiwuwar dawo da shi APC
  • Sai dai kuma, rashin ganin Kwankwaso a jerin ministocin karshe da aka saki ya ba da mamaki, lamarin da yasa majiyoyi suka yi karin haske a wannan rahoton

Abuja - Akwai alamu masu karfi da suka nuna cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin daya daga cikin ministocinsa.

Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban Kwankwasiyyar sau biyu, wanda daga baya shima ya tabbatar da cewar suna tattaunawa kan yiwuwar yin aiki tare da shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Abu Daya Tak Da Zai Yi Wa Alkalai Don Gurgunta Cin Hanci A Najeriya, Ya Yi Bayani

Tinubu tare da Kwankwaso
Mukamin Minista: Dalilin Da Yasa Shugaban Kasa Tinubu Ya Ajiye Kwankwaso, Majiyoyi Sun Bayyana Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

An tattaro cewa yunkurin na daga cikin kulla-kullan Tinubu na samun goyon bayan tsarin siyasar jigon na NNPP da kuma yiwuwar dawo da shi cikin APC mai mulki.

Sai dai kuma, ga mamakin mutane da dama, Kwankwaso bai samu shiga jerin ministocin 48 da shugaban kasar ya saki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso: Babu ma'ana a karfafa yan adawa

Wani rahoto jaridar The Guardian ya ambato majiyoyi na cewa, shugaba Tinubu ya ki amincewa da ra'ayin nada Kwankwaso a cikin majalisarsa ne saboda ya yi imanin cewa babu wata ma'ana karfafa yan adawa, wadanda a karshe za su yi amfani da karfin da suke da shi wajen yakarsu.

Rahoton ya kara da cewa shugaban kasar ya kuma karaya kan yadda sabuwar gwamnatin NNPP ta Kano ta ruguza gine-ginen gwamnati da gwamnatin Ganduje ta gina.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

Legit.ng ta tattaro cewa daraktan labarai na hedkwatar APC na kasa, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa akwai yiwuwar farmakar tarihin da Ganduje yabari a Kano ne yasa Kwankwaso bai samu shiga majalisar Tinubu ba.

Jigon na APC ya ce:

"Kwankwaso babban bango ne da za a jingina da shi a siyasar Kano. Amma hanya da yanayin yadda tafiyar Kwankwasiya ke tafiyar da kanta yasa goyon bayan da Kwankwaso ke da shi ya dunga raguwa sannu a hankali.
"Hakan kuwa ya faru ne saboda irin gaggarumin hargitsin da kungiyar ke kawowa a siyasar Kano, da kuma karawa Najeriya.”

Tinubu ya sa labule da Kwankwaso

A wani labarin, mun ji cewa jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi wata ganawa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kamar yadda hadimin tsohon gwamnan ya bayyana a dandalin X, ‘yan siyasar sun hadu ne a yammacin ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng