Shugabannin Jam'iyyar NNPP Na Jihohi Sun Yi Fatali Da Dakatar Da Shugaban BoT na Jam'iyyar
- Dakatar da shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), bai yi wa.shugabannin jam'iyyar na jihohi daɗi ba
- Shugabannin sun yo fatali da dakatarwar da ƴan kwamitin NWC suka yi wa Dr Boniface Aniebonam inda suka buƙaci a gaggauta soke ta
- Shugabannin sun yi kira ga jagoran jam'iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso da ya ja kunnen ƴan amshin shatansa da ke a NWC
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - Shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihohi, sun yi watsi da dakatar da shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, Dr Boniface Aniebonam, da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar ya yi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabansu kuma shugaban jam'iyyar na jihar Kwara, Abdulsalam AbdulRasaq ya rattaɓawa hannu, rahoton Leadership ya tabbatar.
A cikin sanarwar wacce AbdulRasaq ya rabawa manema labarai ranar Juma'a a birnin Ilorin, ya bayyana dakatar da Aniebonam a matsayin abin da bai dace ba wanda ba za su amince da shi ba.
Shugabannin sun ja kunnen Kwankwaso
A yayin da ya buƙaci a soke umarnin dakatarwar, AbdulRazaq ya yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya jan kunnen ƴan barandansa da ke a cikin NWC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cikin sanarwar shugabannin sun nuna kaɗuwarsu da rashin amincewa da dakatar da Dr Boniface Aniebonam da ƴan kwamitin NWC na jam'iyyar suka yi.
Shugabannin sun bayyana matakin da ƴan kwamitin suka ɗauka a matsayin wanda bai dace ba kuma ya saɓawa kunɗin tsarin mulkin jam'iyyar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Muna kiran da a gaggauta soke umarnin dakatar da Dr Aniebonam, wanda ba wau kawai ya kafa tubalin ginin jam'iyyyar NNPP ba ne, amma ya yi rainon jam'iyyar har na shekara 20 domin kawo ta matsayin da take a yanzu."
"A dalilin hakan ne mu ke kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen shekarar 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yaja kunnen ƴan amshin shatansa da ke cikin NWC."
Ganduje Ya Magantu Kan Rikicin APC
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar All Progressives na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar kan rabon muƙaman NWC.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin shawo kan matsalar wacce ya bayyana a matsayin matsalr cikin gida.
Asali: Legit.ng