Jerin Sunaye: Gwamna Aliyu Ya Raba Wa Sabbin Kwamishinoni Muƙamai a Sokoto
Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya raba muƙamai ga sabbin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwan da ya rantsar ranar Talata, 22 ga watan Agusta.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Abubakar Bawa ya fitar kuma ta shiga hannun manema labarai.
Gwamna Aliyu ya yi wa sabbin kwamishinonin guda 25 fatan nasara a aikin da suka tasa a gaba na yi wa al'ummar jihar Sakkwato da gwamnati aiki, Ripples ta rahoto.
Jerin kwamishinoni 25 da mukaman da gwamna ya ba su
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen kwamishinoni 25 da suka karbi rantsuwar kama aiki a jihar Sakkwato da kuma ma'aikatun da aka tura su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Nasiru Muhammad Binji - Ma'aikatar shari'a kuma Antoni Janar na jihar Sakkwato
2. Ibrahim Adare - Ma'aikatar kananan hukumomi
3. Idris Gobir (Mataimakin gwamna) - Ma'aikatar ayyuka
4. Muhammadu Jabbi Shagari - Ma'aikatar kuɗi
5. Sharehu Abubakar Kamarawa - Ma'aikatar harkokin cikin gida
6. Alhaji Muhammad Tukur Alkali - Ma'aikatar ilimin farko da na sakandire
7. Sheikh Dakta Jabir Mai Hula - Ma'aikatar harkokin addinai
8. Nasiru Tsoho - Ma'aikatar filaye da gidaje
9. Aminu Abdullahi (Iyan Sakkwato) - Ma'aikatar ilimin gaba da sakandire
10. Hadiza Shagari - Ma'aikatar harkokin mata da ƙananan yara
11. Sambo Bello Ɗanchadi - Ma'aikatar yaɗa labarai
12. Alhaji Bello Muhammad Wamakko - Ma'aikatar noma.
13. Jamilu Umat Gosta - Ma'aikatar matasa da wasanni
14. Bala Kokani - Ma'aikatar kimiyya da fasaha
15. Yusuf Muhammad Macciɗo - Ma'aikatar ruwa
16. Hajiya Asabe Balarabe - Ma'aikatar lafiya
17. Nura Shehu Tangaza - Ma'aikatar mahalli
18. Shehu Chacho - Ma'aikatar ayyuka na musamman
19. Ya’u Umar Danda - Ma'aikatar jinƙai da walwalar al'umma
20. Aminu Magaji Bodai - Ma'aikatar al'adu da wuraren buɗe ido
21. Haruna Umar Bashar - Ma'aikatar kasuwanci, ciniki da masana'antu
22. Bashar Abbas Kwabo - Ma'aikatar kirkire-kirkire da tattalin arziƙin zamani
23. Sanusi Ibrahim Umar - Ma'aikatar wuta da albarkatun man fetur
24. Alhaji Isah Tambagarka - Ma'aikatar haɓaka ma'adanan ƙasa
25. Aliyu Abubakar Tureta - Ma'aikatar bunƙasa kiwon dabbobi da kifi.
Gwamnatin Delta Ta Rage Wa Ma'aikata Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3
A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Delta ta bayyana matakan da ta ɗauka domin rage wa mutane zafin cire tallafin man fetur.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya ce gwamnatinsa ta amince da ƙara wa ma'aikata N10,000 domin agaza musu a wannan yanayi da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng