‘Zan Sauya Sunan Diyata Zuwa Na Mahaifiyar Tinubu', Wani Mutumin Bauchi Ya Ci Alwashi
- Wani mutumin Bauchi ya bayyana sharadi guda da zai sa ya sauyawa diyarsa suna zuwa na mahaifiyar shugaban kasa
- Khamis Musa Darazo ya sha alwashin mayar da sunan diyarsa zuwa Abibat idan har Bola Tinubu ya yi nasara a kotun zaben shugaban kasa
- Darazo ya ce zai yi haka ne domin nuna godiya ga Allah da ya tabbatar da nasarar shugaban Najeriyan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Shugaban kungiyar wayar da kan matasan Arewa kan shugabanci da zabe a jihar Bauchi, Khamis Musa Darazo, ya sha alwashin sauya sunan diyarsa mai shekaru biyu zuwa na mahaifiyar shugaban kasa Bola Tinubu idan har ya yi nasara a kotun zabe.
Darazo wanda ya zanta da manema labarai a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, a Bauchi ya nuna karfin gwiwar cewa Tinubu zai yi nasara a kan Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP a kotun zaben, jaridar Vanguard ta rahoto.
Zan sauya sunan diyata zuwa Abibatu mahaifiyar Tinubu, matashi dan Bauchi
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Shawarar da na yanke na sauya sunan diyata zuwa Abibatu shine don nuna godiya ga Allah kan tabbatar da zaben Tinubu.
“Wannan ya kuma kasance ne don tabbatar da cewar Bola Ahmed Tinubu mutum ne wanda ke tabbatar da ganin cewa kowa ya samu na kaiwa bakin salati. Ya kuma kasance magidanci wanda ya dasa ginshiki mai karfi a bangaren zamantakewa, tattalin arziki da siyasar Najeriya, Afrika da ma kasa baki daya.”
Khamis Musa Darazo ya kuma yabama Tinubu kan sake nada Malam Ya’u Shehu Darazo a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan siyasa da harkokin gwamnati bayan ya yi aiki da Buhari a matsayin babban mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka na musamman.
Ya alakanta nadin Ya’u ga jajaircewarsa ga kasar, arewa maso gabas, Bauchi da kuma mahaifarsa ta Darazo, rahoton Leadership.
Abubuwan da Hadimin Tinubu, Darazo ya yi wa matasa
Ya kuma bayyana cewa tun bayan kafa APC a matsayin jam'iyyar siyasa, dattijon kasar ke ta aiki ba ji ba gani don samar da romon damokradiyya ga yan Najeriya musamman mutanen Darazo.
Ya tuna cewa tun bayan nada Ya’u Darazo har zuwa yanzu, ya bayar da tallafin karatu kyauta ga matasa 200 a fadin kasar domin su ci gaba da karatunsu, ya taimaki matasa da dama da jari don bukasa kasuwancinsu.
Kalamansa:
“Malam Ya’u Darazo ya ba kamfanin Powehill Construction LTD ayyukan gyaran hanyoyi da magudanar ruwa a mahaifarsa da ya kai N897,577, 627.79k. Ya taimaka wajen samar da tashar samar da wutar lantarki a Darazo domin bunkasa wutar lantarki tare da gyara masallatan Juma’a na Darazo da Konkiel.
Ya kuma bayyana cewa, Ya’u ya kawo kwalejin ilimi a karamar hukumar Darazo da nufin ba da dama ga matasa masu karamin karfi ta yadda za su samu damar yin karatu mai zurfi.
Har ila yau, ya kuma ba da kwangilar aikin madatsar ruwa don karfafa wa matasa gwiwa wajen yin noman rani, da kuma samawa mutum sama da 50 da suka kammala karatun digiri mukamai a hukumomin gwamnati daban-daban da sauransu.
Ministar Tinubu ta durkusa har kasa don gaishe shi
A wani labarin, mun ji cewa Lola Ade-John, sabuwar ministar yawon bude ido da aka rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, ta shiga kanen labarai.
Hakan ya kasance ne yayin da Ade-John ta je gaishe da shugaban kasar Najeriya a inda yake zaune, a wajen rantsar da sabbin ministoci da aka yi a fadar shugaban kasa Abuja.
Asali: Legit.ng