"Peter Obi Ne Zai Yi Nasara a Kotu" Babban Malami Ya Faɗi Wahayin da Aka Masa
- Har yanzu akwai sauran rina a kaba a ƙarar da Peter Obi da LP suka kalubalanci nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- A ƙarar, Obi ya roki Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban ƙasa ta soke nasarar Tinubu bisa zargin magudin zaɓe ranar 25 ga watan Fabrairu
- Wani malamin coci, Fasto Kingsley Okwuwe, ya bayyana wahayi inda ya yi hasashen nasara ga ɗan takarar Labour Party
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Fasto Kingsley Okwuwe na cocin 'Revival and Restoration Global Mission' ya ce Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ne zai samu nasara a Kotu.
Fitaccen Malamin ya yi hasashen cewa kotun zabe (PEPC) zata rushe nasarar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Allah ya faɗa mun Obi zai yi nasara - Fasto
Idan baku manta ba, shugaba Tinubu ya lallasa sauran 'yan takarar shugaban ƙasa guda 17 da suka gwabza a zaɓe. Ya samu kuri'u 8,794, 726 wanda suka ba shi nasara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da sakamakon zaben bayan kammala tattara wa a birnin tarayya Abuja.
Ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya zo na biyu da ƙuri'u 6,984, 520.
Peter Obi ne ya zo na uku a zaben da ƙuri'u 6,101,533 yayin da Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya zo na huɗu da kuri'u 1,496,487.
Atiku da Obi sun garzaya Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa sun kalubalanci nasarar Bola Ahmed Tinubu.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa shafin cocinsa na Youtube, Fasto Ukwuwe ya ce:
"Allah ya gaya mun cewa Peter Obi ne zai samu nasara a Kotun zaɓe. Wasu daga cikinku zasu yi tantamar ta ya haka zata faru? Alkalai, wannan da wancan."
"Allah dai ya ce Obi ne zai samu nasara a Kotu kuma ku jira ku gani, zai zo ya wuce."
Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Kalubalanci Nasarar Dauda Lawal
A wani rahoton kuma Kotun zaɓe ta shirya yanke hukunci kan karar da Matawalle ya kalubalanci nasarar gwamna Lawal na Zamfara.
Kwamitin alƙalai uku na Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Cordelia Ogani ya ce za a sanar da kowane bangare ranar da kotu zata bayyana hukunci nan gaba,
Asali: Legit.ng