Zamfara: Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Kalubalanci Nasarar Dauda Lawal

Zamfara: Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Kalubalanci Nasarar Dauda Lawal

  • Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta tanadi hukunci kan ƙarar da ta kalubalanci nasarar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal
  • Mai shari'a Cordelia Ogadi, wanda ke jagorantar shari'ar, ya ce Kotu zata sanar da kowane ɓangare ranar bayyana hukuncinta nan gaba
  • Tsohon gwamna, Muhammad Bello Matawalle, ne ya shigar ƙara gaban Kotun inda ya kalubalanci nasarar gwamna Lawal

Sokoto state - Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan jihar Zamfara mai zama a Sakkwato ta tanadi hukunci kan ƙarar da ta kalubalanci nasarar gwamna Dauda Lawal.

Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ne ya shigar ƙara gaban Kotun yana kalulantar sahihancin sakamakon zaben gwamna wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Bello Matawalle da Gwamna Dauda Lawal.
Zamfara: Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Kalubalanci Nasarar Dauda Lawal Hoto: Bello Matawalle/Dauda Lawal
Asali: Facebook

Kotu zata zaɓi ranar yanke hukunci

Kwamitin alƙalai uku na Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Cordelia Ogani ya ce za a sanar da kowane bangare ranar da kotu zata bayyana hukunci nan gaba, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar a Jihar Arewa Kan Abu 1

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lauyan Matawalle, Barista Usman Sule, ya ce hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ba ta sanya sakamakon ƙaramar hukumar Maradun ba, mai ƙuri'u 98,564.

Sule ya ƙara da faɗa wa Kotun cewa INEC ta yi gaban kanta ta bayyana wanda ya lashe zaɓen gwamna duk ba a kammala kaɗa kuri'a a wasu mazaɓun jihar ba.

Gwamna Lawal ya nemi Kotu ta kori ƙarar

A nasa ɓangaren, gwamna Dauda Lawal ya buƙaci Kotun ta kori ƙarar da Matawalle ke kalubalantar nasarar da ya samu saboda ba ta cancanta ba.

Gwamnan, INEC da jam'iyyar PDP sun kafa hujja da shari'ar da ta wakana tsakanin gwaman Ademola Adeleke na jihar Osun da tsohon gwamna Oyetola.

Sun ƙara da cewa Matawalle ya gaza gamsar da Kotu da kwararan hujjojin, bisa haka suka roƙi Kotun ta yi fatali da ƙarar baki ɗaya, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wahayi Daga Allah: Fitaccen Malami Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara a Kotu Tsakanin Atiku da Peter Obi

PDP ta kafa kwamitin rikon kwarya a Kogi

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta naɗa shugaban jam'iyya na rikon kwarya a jihar Kogi da Sakatare bayan karewar wa'adin zababbun mambobin NWC.

Sakataren tsare-tsare, Umar Bature ne ya sanar da haka, inda ya bayyana sunayen mambobin kwamitin rikon kwarya mai ɗauke da mutum 14.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262