Tinubu: "Ba Zamu Faɗi Karya Domin Kare Gwamnati Ba' Sabon Minista

Tinubu: "Ba Zamu Faɗi Karya Domin Kare Gwamnati Ba' Sabon Minista

  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris ya shiga Ofis a karon farko bayan rantsuwar kama aiki ranar Litini
  • Idris ya bayyana cewa ma'aikatarsa ba zata rungumi yin ƙarya ba domin kare gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Hannatu Musawa, ministar al'adu da fikirar tattalin arziki ta sha alwashin ƙara samar da kudin shiga ga Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Sabon ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Muhammed Idris, ya ce ma'aikatarsa ba zata yi wa 'yan Najeriya ƙarya domin kare gwamnati ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ministan na cewa maimakon haka, "Zamu riƙa bayyana wa al'umma gaskiya a ko da yaushe."

Sabbin Ministocin shugaban ƙasa.
Tinubu: "Ba Zamu Faɗi Karya Domin Kare Gwamnati Ba' Sabon Minista Hoto: Muhammed Idris, Barrister Hannatu Musawa
Asali: Facebook

Ministan ya yi wannan furucin ne a sa'ilin da ya shiga Ofis karon farko bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da shi a Abuja ranar Litinin, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan Tinubu Ya Rantsar Da Wike a Matsayin Ministan Abuja

Ya ce ma'aikatar yaɗa labarai da gwamnatin shugaba Tinubu za su faɗi gaskiya ta yadda mutane za su aminta da su a duk lokacin da za a fitar da wani bayani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon ministan ya bayyana cewa gwamnati zata duba duk inda ta yi kuskure a baya kana ta yi kokarin gyara wa da kuma daidaita inda ya kamata.

Muhammed Idris ya ce wayar da kan al'umma na ƙasa zai shiga sahun manyan ginshiƙan da gwamnatin tarayya zata bai wa fifiko, bisa haka, "Nan da wasu kwanaki zamu sanar da shirye-shiryen mu ga yan Najeriya."

Haka zalika ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji duk wani nau'in labaran ƙanzon kurege kuma su riƙa tantance sahihin bayani kafin yaɗa wa a jama'a.

A cewarsa, ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kan al'umma zata zama mai sauke nauyi kuma a bude ga 'yan Najeriya a karƙashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Femi Falana Ya Bukaci Tinubu Ya Saki Abdulrasheed Bawa, Ya Bayar Da Kwararan Dalilai

Hannatu Musawa ta shiga Ofis

A nata ɓangaren, Ministar zane-zane, al'adu da fikirar tattalin arziƙi, Hannatu Musawa ta ce zata ƙara ɗaga Najeriya a idon duniya kuma zata samar da kuɗaɗen shiga ga FG.

Ta ce ma'aikatar zata yi duk mai yiwuwa wajen sauya kallo mara kyau da ake wa ƙasar nan a duniya.

Musawa ta bayyana cewa yana da muhimmaci a dawo da haɗin kan ƙasa, wanda shi ne babban burin iyayen ƙasa da suka yi fafukar ganin Najeriya ta tsaya da ƙafafunta.

Babban Jigo Ya Maka Mukaddashin Shugaban Jam'iyya a Gaban Kotu

A wani rahoton kuma Rigingimun cikin gida da suka yi wa jam'iyyar PDP katutu sun sake buɗe sabon shafi kan batun shugaban jam'iyya na ƙasa.

Babban jigo a jam'iyyar PDP , Daboikiabo Warmate, ya maka muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagun a gaban Kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262