Dan Majalisar APC Ya Nuna Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa

Dan Majalisar APC Ya Nuna Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa

  • Akin Alabi, wani ɗan majalisar wakilai na APC mai wakiltar Egbeda/Ona Ara daga jihar Oyo, ya bayyana cewa zai yi takarar shugaban nan gaba
  • Ɗan majalisar wakilan ya bayyana cewa idan lokacin yin takararsa ya yi, waɗanda ya koyar kan harkokin kasuwanci za su bayar da shaida a kansa
  • A matsayinsa na mawallafin littattafan kasuwanci, ɗan majalisar ya nuna farin cikinsa kan yadda waɗanda ya koyar har sun fara vin gajiya

Ibadan, Oyo - Akin Alabi, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan majlisar wakilai mai wakiltar Egbeda/Ona Ara daga jihar Oyo, ya bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa a nan gaba.

Ɗan majalisar wanda ya wallafa litattafai masu yawa kan kasuwanci sannan ya koyar da ƴan kasuwa, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 15 ga watan Agusta a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

"Abun Kunya": 'Yan Najeriya Sun Fusata Bayan Ganin Dakarun Tsaro Na Musamman Da Ke Gadin Seyi Tinubu

Akin Alabi ya bayyana aniyar yin takarar shugaban kasa
Alabi ya bayyana aniyar yin takarar shugaban kasa Hoto: @akinalabi
Source: Twitter

A cewar ɗan majalisar, mutanen da ya koyar kan harkokin kasuwanvi za sj bayar da shaida a kansa idan lokacin takararsa ta neman shugaban ƙasa ya yi.

Dalilin yin takarar Alabi

Ɗan majalisar ya gabatar da ƙudirori masu yawa a majalisa waɗanda suka haɗa da na hana hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta ƙasa (FIRS) daga karɓar haraji kan cinikayyar yanar gizo, da kuɗirin soke rundunar ƴan sanda ta Special Anti-Robbery Squad (SARS)

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Talata, ɗan majalisar ya bayyana cewa:

"Ina samun labarai masu daɗi daga wajen matasan nan dana koyar kan kasuwanci a watan da ya gabata. Lokacin da na ke son zama shugaban ƙasa, zan samu goyon baya da shaida mai yawa."

Alabi, wanda shi ne ya kafa wani shahararren kamfanin caca a Najeriya, ya lashe zaɓen ɗan majalisa ne a shekarar 2019 bayan ya bar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Hukumomi a Jihar Kano Sun Bayyana Kwakkwaran Dalilin Cafke Masu Siyar Da Maganin Gargajiya

Tinubu Ya Nada Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon babban sakataren fadar shugaban ƙasa.

Olufusan Adebiyi wanda ya fito daga jihar Ekiti, ya maye gurbin Tijjani Umar wanda ya yi ritaya bayan wa'adin cikar lokacin aikinsa ya cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng