Gwamnan Jihar Imo Ya Bayyana Abokiyar Takararsa a Zaben Gwamnan Jihar Mai Zuwa

Gwamnan Jihar Imo Ya Bayyana Abokiyar Takararsa a Zaben Gwamnan Jihar Mai Zuwa

  • Gwamnan jihar Imo ya bayyana abokiyar takararsa a bainar jama'a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamna Hope Uzodinma ya aje mataimakinsa na yanzu a gefe guda inda ya zaɓo Lady Chinyere Ihuoma Ekomaro
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya zaɓo Ekomaro ne saboda lissafin siyasar jihar da ya sauya ba don yana da matsala da mataimakinsa ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya sanar da Lady Chinyere Ihuoma Ekomaro a matsayin abokiyar takararsa a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba mai zuwa.

Uzodinma, wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen, ya bayyana abokiyar takarar tasa ne a birnin Owerri, babban birnin jihar ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, cewar rahoton Daily Trust.

Gwamnan Imo ya zabo mace a matsayin abokiyar takara
Gwamna Uzodinma ya zabo mace a matsayin abokiyar takararsa a zaben gwamnan jihar Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa gwamnatin APC ita ce ta fi dacewa ta ci gaba da inganta rayuwar al'ummar jihar domin samar da ci gaban da ya dace.

Kara karanta wannan

Hankalin Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP Ya Tashi Bisa Zargin Yunkurin Yi Ma Sa Juyin Mulki

Gwamnan ya bayyana cewa a lokacin yaƙin neman zaɓe yana so ayyukan da ya gudanar su yi masa yaƙin neman zaɓen, rahoton PM News ya tabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A yau na zayyano kaɗan daga cikin nasarorin da mu ka samu domin sanar da mutanen jihar Imo cewa gwamnatin APC ita ce ta fi dacewa wajen samar da ci gaban da mu ke buƙata."
"Don haka a lokacin yaƙin neman zaɓen sake ɗarewa kan kujerar mulki, ina so ayyukan da na yi su yi min yaƙin neman zaɓen. Al'ummar jihar Imo da na sani sun yaba da ayyukan da mu ka gudanar a watanni 43 da suka gabata."
"Ba mu buƙatar yin wasu ƙulle-ƙulle, farfaganda da yaudara domin a sake zaɓen mu. Wannan aikin ƴan adawa ne waɗanda ba su da takamaiman abin da za su faɗa."

Kara karanta wannan

An Samu Rikici Tsakanin APC Da PDP Kan Kwamishinoni a Majalisar Dokokin Jihar Arewa

Meyasa Uzodinma ya zaɓo Ekomaro?

Ya bayyana zaɓo Ekomaro da ya yi ba yana nufin cewa yana da matsala da mataimakinsa na yanzu Placid Njoku, ba ne amma ya zaɓo abokiyar takararsa ne saboda lissafin siyasar jihar da ya sauya.

Gwamnan ya kuma bayar da tabbacinsa wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana. Uzodinma ya yi amanna cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wajen kare rayuka da dukiyar al'umma duk da matsalar tsaron da aka samu a jihar.

Uzodinma Ya Kara Albashin Ma'aikata

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya yi wa ma'aikatan jihar ƙarin albashi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamnan ya ƙarawa ma'aikatan N10,000 a albashinsu biyo bayan tsige tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng